A
wancan makon mun kawo maku rahoton yadda wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello ta
Zariya mai suna Shettima Ali Kyari ya kera jirgin sama-mai yawo ba tara da
matuki ba. Wannan karo Muhammad Malumfashi daga NAIJ Hausa ya samu damar zama
da shi musamman domin jin ainihin yadda abin yake.
Ko da na samu ganawa da
Shettima, sai ya mani bayani cewa wannan aikin jirgin, hadaka ne, shi da wasu
abokan karatun sa; Aliyu Tanimu Muhammad da kuma Abdurrazak Abdurraheem. Wannan
dalibai uku (wadanda ake kira da 3 Idiots a Makaranta) sun yi wannan aiki ne a
matsayin kundin digirin su na farko a fannin Ilmin kimiyyar ’Physics’ a Jamiar
Ahmadu Bello, Zaria. Shettima ne wanda ya dauki nauyin aikin lantarki-wanda
dama can yana da diploma a fannin wutan lantarki daga Makarantar Nuhu Bamalli,
shi kuma Aliyu Tanimu Muhammad ya dauki nauyin aikin kere-kere da kuma kayan da
ya kamata ayi amfani da su, Abdurrazak ya dauki nauyin tada jirgin sararin
samaniya da kuma sauran bincike.
Shettima ba bako bane a
harkar Jiragen sama, ko Firamaren sa dai a makarantar Aviation Staff School yayi, makarantar koyar da tukin Jirgin Sama a
Najeriya, ya kuma yi kwas na watanni a Bangaren kula da Jirgin Saman a
Makarantar koyon tukin jirgi ta Zariya-tare da daya daga cikin abokan aikin sa,
Aliyu Tanimu Muhammad. Shettima ya dade yana burin kera jirgin sama, kamar
wanda zai zama yana sintiri, yana yawo domin kula da Makarantar su ta ABU da ke
Zariya, yace hakan zai yi maganin barayi. Mahaifin sa, wanda Injiniya ne a
Makarantar koyon tukin jirgi, ya tabbatar masa da cewa hakan ba zai gagara ba.
Watau a samu jirgi mara direba, mai kuma dauke da na’urar daukar hoto da kuma
abin daukar Magana, kai har da ma na’urar da ke gane hayaki.
Abin kamar wasa, sai ga
jirgi ya tashi wancan makon, an gwada sa lafiya lau a Filin wasanni na Jami’ar
ta Ahmadu Bello ta Zariya. Wannan jirgi ya tashi a gaban Malamin da ke kula da
wannan aiki Dr. AA AbdelMalik da kuma Shugaban sasshen ‘Physics’ Dr. YI Zakari
da ma wasu dabam da suka shaida. Anyi aikin kera wannan jirgi ne a dakin karatu
na sashen Mechatronics da ke Jami’ar ta ABU Zariya, wani kwararre a wajen,
Malam Aliyu ya taimaka sosai wajen ganin yiwuwar wannan aiki. Abin ban sha’awa
shine su Kyari sun hada wannan jirgi ne da kayan gida; irin su karfen labule,
gwangwani, soso, langa-langa, kwali, katako dsr. Fiffiken jirgin na wani irin kwali
ne maras nauyi, cikin sa kuma akwai wani dan guntun katako domin tsaida shi
kikam a iska idan ya tashi. Kai, har tayan jirgin kuwa yana dauke ne da
gwangwanin lemu na ‘Coke’ da kuma
wani soso, saboda a samu dadin sauka a Kasa. Abin dai sai wanda ya gani. Wani
Jami’in makarantar koyon tukin Jirgi da ke Zariya, wanda masani ne a harkar,
Mista Chiwaitalu O. Tijjani ya taimaka wajen samar da wasu kayan da ake bukata,
irin su Injin jirgin; wanda na DC Motor
ne, abin da suke kira RC ko Radio Control.
Shettima asalin sa Babarbare
ne daga jin sunan sa, Tanimu kuma dan kabilar Kakanda ne, shi kuma Abdulrrazak
bayarabe ne, amma kusan duk suna zaune a Zariya. Watakila hakan ta sa Shettima
ya sanyawa wannan jirgi suna HopeForChibokGirls, watau dai da rabon ganin yaran
na Chibok da Yan Boko Haramnan suka sace. A cewar Shettima, ya zama dole kowa
yayi hobbasa a Kasar kamar dai yadda aka ce ChangeBeginsWithMe ma’ana canji ya
fara daga kashin kai na. Shettima yace ya ga ya dace suyi abin da ya wuce
zallan kira kamar BBOG, yace a matsayin su na daliban makaranta, suka ce bari
su hada abin da zai taimakawa Najeriya.
A wani lokaci da su Shettima
suka je yawon bude ido daga makarantar su zuwa NIG com Sat, masu kula da
na’urar tauraron dan adam na Najeriya da ke samaniya, sai ya fahimci ashe yana
yiwuwa a kera irin wannan jirgi da zai taimaki bil adama, ba wai kawai aikin sa
wutar yaki ba. Ko don nan gaba, musamman shi Shettima Ali Kyari, yana da burin
fadada wannan aiki. Irin wannan jirgi zai iya jiwo kanshin hayaki daga nesa, ya
kuma bada shela a dakin lura, ya kuma zama yana iya daukar hoto yayin da yake
tafiya, hakan za ta sa a gane duk inda ya ke. Bugu da kari kuma ya zama yana
dauke da na’urar jin sautin magana. Idan an samu yadda ake so, sai wannan jirgi
ya je Kaduna ya dawo ba tare da wani ya tuka sa ba. Tirkashi.
A karanta sauran bayanai a shafin mu na NAIJ Hausa: https://hausa.naij.com/992032-babban-labari-yadda-daliban-abu-zaria-suka-kera-jirgi.html
Ana iyo biyo ni a zauren twitter @ya_waliyyi.
Nagode.
No comments:
Post a Comment