Wani mutumi ya kori Amaryar sa bayan ya gano mummuna ce
– Wani Balarabe ya rabu da ‘Yar Amaryar sa jim kadan bayan daura aure
– Angon yace ya gano ashe Amaryar ta sa ba ta da kyau idan ta cire kwalliya
Wani Balarabe ya saki ‘Yar
Amaryar matar sa jim kadan da yin aure bayan ya gan ta ba tare da kwalliya ba a
karo na farko. Dakta Abdul Azeez Azif Asaf mai shekara 34 ya rabu da amaryar sa
‘Yar shekara 28 bayan da ya ga fuskar ta ba tare da kayan shafa ba.
Dakta Abdul Azeez Azif yace
Amaryar ta yaudare sa da kayan shafe-shafe. Asalin abin da ya wakana dai shine,
ango Abdul Azeez ya kai matar sa teku domin wasa da ruwa, ko da ta shiga ta
fito sai ya ga abubuwa sun canza, ba dai kamar yadda ya saba ganin ta ba. Yace
bayan ruwa ya wanke mata fuska sai ya ga kamar ba ita ba.
Abdul Azeez Azif yace ashe
Amaryar ta sa tana sanya gashin ido da girar karya ne sannan kuma an yi mata
aiki domin a rikida mata siffa kafin tayi aure. Yace sam bai gane Amaryar ba ko
da ta shi ga ruwa ta fito.
Likitan wannan Amaryar yace
tayi niyyar fadawa mijin ta abin da ya faru, sai dai ta makara. Yanzu haka dai
sun rabu, mijin yace fau-fau ba zai yarda ba.
[Daga GULF news]
No comments:
Post a Comment