Ana rikicin limanci a Masallacin Sultan Bello
An tsaida Sallar Jumu’a saboda rikicin limanci a Sultan Bello
Rikicin Limanci ya barke a Babban Masallacin nan na Sultan Bello da ke Kaduna
‘Yan Sanda sun harba bindiga ana tsakar Sallar Juma’a
An yi Sallar Jumu’a kashi biyu a Masallacin
Rikicin Limanci ya barke a
Babban Masallacin nan na Sultan Bello da ke Kaduna. Abin har ta kai an katse
Sallar Juma’a a Masallacin Jiya. Har dai sai da Jami’an tsaro suka shigo cikin
lamarin gudun kar a saba doka.
Wani wanda a gaban sa aka yi
komai ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Na’ibin Limamin Masallacin ya
gabatar da huduba kamar yadda aka saba, ya tashi ya fara bada Sallah, kwatsam
kawai sa aka yi kokari a hana sa jan Sallar a Ra’aka ta farko, daga nan ne Jami’an
‘Yan Sanda suka shiga harbar bindiga da borkonon tsohuwa a cikin masallaci
Bayan Jami’an tsaro sun
shiga harbi ne, sai kowa ya tsere daga Masallacin, daga nan kuma mutanen dayan
Limamin watau Dr. Khalid suka shiga suka fara nasu Sallar Jumu’ar. Bayan dai
sun fara kenan wasu matasa suka shigo Masallacin suka hana su Sallar, don dole
suka tashi.
Jami’in ‘Yan Sanda ASP Aliyu
Usman ya tabbatar da faruwar wannan rikici a Babban Masallaci na Sultan Bello.
An dai jima ana Rikicin Limanci a Masallacin. Su dai ‘Yan Sanda
sun ce rayuka suke karewa ba Liman suka nada ba.
No comments:
Post a Comment