Dama SIDA na da magani?
Da alamu dai Turawa na daf
da gano maganin cutar nan mai karya garkuwar jikin bil adama wanda aka sani da
Kanjamau, a Turance kuma ana kiran ta HIV AIDS. Huffington Post ta rahoto cewa
yanzu haka har an yi wa wani ma’aikaci a Kasar Birtaniya magananin wannan cuta,
kuma har ya warke.
Bayan an yi wasu dabaru
sai ga shi an samu wannan maras lafiya ya murmure, cutar ta fice daga jikin sa.
An dai yi wa wannan mutumi wata allura ne, wanda ta gano kwayoyin cutar, daga
nan kuma aka yi amfani da wani magani mai suna Vorinosat, hakan ya taimaka
wajen kashe cutar daga jikin sa.
Shi wannan magani na
Vorinosat, ana amfani da shi wajen maganin cutar Cancer, yana kokari wajen kashe duk wasu kwayar rai da suka kamu da
cuta. Masana dai sun ce wannan maganin ya dauko hanya wajen kawo karshen wannan
masifaffen cuta a duniya. Haka kuma yanzu ana kokarin gwado karfin sa ne. Yanzu haka dai ana bukatar
auna karfin wannan magani a jikin mutane 50, wanda zai bada damar gane karfin
maganin idan har dukkanin su kowa ya warke.Cutar HIV idan ta zama AIDS dai tana
karya garkuwar jikin dan adam. Kawo yanzu dai ba ta da wani magani a duniya.
Muhammad Malumfashi ya tsakayo daga wani shafi ya fassara
No comments:
Post a Comment