‘Yar wasan kwaikwayo ta zama barauniya
Ana zargin wata 'Yar
wasan kwaikwayo da aka sani ta Nollywood mai suna Joy Anyim da laifin sata a Garin Uyo
na Akwa-Ibom. Ana zargin ‘Yar wasan kwaikwayo Joy Anyim da satar makudan kudi
kusan Naira rabin miliyan.
Gidan yada labarai na Jihar Akwa-Ibom
din AKBC ta bayyana wannan abin kunya a wannan mako. Wasu manyan gidajen jarida
ma na Jihar sun kawo labarin yadda ake zargin wannan tauraruwar ‘Yar wasan
kwaikwayo da satan Naira dubu dari hudu da sittin N460000.
Sai dai magoya bayan Joy
Anyim suna ganin cewa wannan labari faufau karya ce kurum, domin ‘Yar wasan
kwaikwayo tana da arziki kwarai, musamman ganin mijin ta mai kudi ne na gaske.
Wanda dai duk ya san wannan jaruma ‘Yar wasan kwaikwayo ya san tana da arziki. To ya akayi haka?
Sai dai yanzu haka har an
bada umarnin a daure wannan ‘Yar wasan kwaikwayo a gidan maza har sai an bada
belin ta na N500,000. Asalin wannan ‘Yar wasa dai ‘Yar Enugu ce, kuma yayin da
ta shiga wannan hali, duk mutanen ta sun watse sun bar ta. An ce maza suka yi ta kashe mata auren ta, har da wani Fasto.
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan labari daga NAIJ.com. Domin samun labarai da dumi-dumin su, Sai a garzaya Shafi na NAIJ
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment