– Hajiya Aisha Buhari, matar Shugaban Kasa tace tana tare da Maigidan ta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
– Matar Shugaban Kasar ta bayyana haka ne yayin da ta kai ziyara Jihar Borno
– Aisha Buhari ta je Garin Benisheik da aka karbe daga hannun Boko Haram, tace ta ji dadin ganin haka
Hajiya Aisha
Buhari, matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tace tana tare da Mai gidan nata
da kuma kokarin ganin nasarar Gwamnatin sa. A kwanakin baya dai Hajiya Aisha
Buhari ta ba duniya mamaki, inda tace idan fa mai gidan nata bai canza salo ba,
to ba da ita nan da 2019. Aisha Buhari tayi wannan maganar ne a Gidan BBC da ke
Landan.
Matar Shugaban Kasar tace
yanzu dai tana tare da mai gidan ta, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin kuwa
ya fara cika wasu alkawuran da ya dauka lokacin yana neman takarar Shugaban
Kasa. Matar Shugaban Kasa, Aisha
Buhari tayi wannan bayani ne lokacin da ta kai ziyara Garin Benisheik da ke
Borno, da aka karbe daga hannun ‘Yan Kungiyar Boko Haram.
Matar Shugaban Kasar
ta raba kayan agaji ga wasu daga cikin matan yankin. Matar Gwamnan Jihar Borno,
Nana Shettima ce ta tare Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari da tawagar ta; ta
matan hafsun Sojojin Kasar da wasu matan ‘Yan Siyasa.
Aisha Buhari ta bayyanawa
mutanen Garin Kaga cewa tayi farin cikin ganin an fatattaki Boko Haram daga
yankin kamar yadda mai gidan ta yayi masu alkawari. Tace tana tare da maigidan
nata a nan don kuwa mutumin kwarai ne, mai fada ya cika.
No comments:
Post a Comment