– Bola
Ahmed Tinubu yayi dan sharhi a cikin littafin Tarihin Shugaba Muhammadu Buhari
– A Jiya ne wani Bature, Farfesa John Baden ya kaddamar
da littafi a game da Tarihin Shugaba Buhari
– Bola
Tinubu ya bayyana yadda Muhammadu Buhari ya zama Shugaban Kasar Najeriya a
littafin
A jiya, 3 ga watan Oktoba,
Farfesa John Baden, wani masanin huldar Kasa-da-Kasa, kuma wanda yayi fice a
Najeriya ya kaddamar da littafin da ya rubuta a game da Muhammadu Buhari.
Farfesa Baden yana da ilmi game Najeriya da kuma Shugabannin na ta. Farfesa John Baden, ya koyar a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya da kuma Jami'ar Bayero ta Kano a baya.
A littafin, marubucin ya
kawo labarin yadda Muhammadu Buhari yayi gwagwarmaya, ya kuma yi wa Kasa
hidima, har ya zama Shugaban Kasa. Baden ya kuma kawo yadda rayuwar Shugaba
Muhammadu Buhari ta ke a gida. Farfesa Baden ya kasa wanna littafi na sa har
gida 3, tare da kashi 24.
Janaral TY Danjuma ne yayi
ta’alikin wannan littafi, ko dai can TY Danjuma maigidan Buhari ne a gidan
Soja, kuma abokin sa ne kwarai. Janar Danjuma mai ritaya yace ba shakka Buhari
ya shiryawa mulkin Kasar nan. A cikin littafin an kawo yadda su Tinubu suka
kafa Jam’iyyar APC. Wajen hada wannan Jami’yya ta mu-zo-mu-gama an yi
gagwarmaya kwarai, kuma an sadaukar da kai. Har aka zabi Muhammadu Buhari a
matsayin dan takarar Shugaban Kasa.
Bola Tinubu wanda jigo ne a
APC ya kuma yi bayanin yadda Farfesa Yemi Osinbajo ya zama Mataimakin Shugaban
Kasar nan. Tinubu yace Osinbajo ya rike masa Kwamishina lokacin yana Gwamna,
Farfesan shari’a ne kuma Fasto na daya daga cikin Cocin da suka fi kowane girma
a Najeriya, hakan zai sa masu kallon Buhari da wata fuska su daina.
Na samu labarin cewa kwanan nan littafin zai shigo kasuwa domin masu bukata su saya.
A jiyan an dai sadaukar da kudin da aka samu wajen kaddamarwa ne ga 'Yan gudun Hijira da ke Jihar Borno.
Muhammad Malumfashi ya kawo wannan rahoto a NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment