Shugaba Muhammadu Buhari zai saki Sambo Dasuki kuwa?
– Da alamu dai Muhammadu Buhari ba zai saki Sambo Dasuki ba duk da Kotun ECOWAS ta bada umarnin hakan
– Sambo Dasuki ya rike Ofishin mai bada shawara kan tsaro lokacin tsohon Shugaba Jonathan
– Gwamnati na zargin sa da laifi har 19, sai dai Kotun ECOWAS tace a sake sa
Da alamu cewa fa Gwamnatin Buhari ba za ta saki Sambo
Dasuki daga dauri ba duk da cewa Kotun ECOWAS ta Nahiyar yankin Yammacin Afrika
ta bada umarnin hakan. Kanal Sambo Dasuki ya rike Ofishin mai bada shawara kan
harkokin tsaro a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan.
Gwamnatin Najeriya na zargin Kanal Sambo Dasuki da
laifuffuka har guda 19; ciki akwai laifin karkatar da biliyoyin kudin makamai
na Kasar da kuma cin amana. Tuni dai Kanal Dasuki yana garkame, sai dai wani
Kotu na ECOWAS; na Yammacin Afrika ya nemi Gwamnatin Najeriya ta saki Sambo
Dasuki. Lauyoyin Sambo Dasuki sun garzaya Kotun Nahiyar ne bayan
da duk kokarin kubutar da shi ta Kotun Najeriya suka ci tura. Ana dai karar
Dasuki a Kotu kusan biyu a Abuja.
A littafin Tarihin Shugaba Buhari wanda Farfesa baden ya rubuta, za a iya
fahimtar cewa zai yi wahala Gwamnatin Buhari ta saki tsohon mai bada shawara kan
harkar tsaron. A babi na 15 na wannan littafi, Shugaba Buhari yace ba abin da
yake fada da ita kamar rashawa, yayi magana game da harkar tsaro a sha’anin
Soji.
Dasuki dai yayi karfi lokacin mulkin Jonathan, daga mai bada shawara har ta kai shi yake da ikon sayen makamai. Gwamnati dai tana zargin cewa an karkatar da kudin makaman Kasar kusan dala miliyan goma sha biyar. Wwannan ya sa Boko Haram ta fitini al'ummar Kasar musamman Arewa.
Sambo Dasuki yana cikin wadanda
suka kifar da Gwamnatin Buhari na Soji a shekarar 1985. Ko anya Buhari zai saki Dasuki? Ministan Shari'a na Kasar dai yace ba za su yi saurin sakin Dasuki ba tukun har sai sun duba shari'ar da Kotun na ECOWAS, sai dai ba a san ya za a kaya ba...
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan rahoto yau a NAIJ.com, a iya bincika:
https://www.naij.com/author/muhammad-malumfashi.html
No comments:
Post a Comment