Yau ga Mutumin da aka daure fiye da sau dubu
Yayin da wasu ke tsoron su aikata laifi, ga wani nan ya aikata laifuffuka ya fi a kirga a duniya
An kama wannan ta’aliki fiye da sau dubu a rayuwar sa
Duk shi kadai, an daure shi sau kusan 1300
Yayin
da wasu ke tsoron su aikata laifi, ga wani nan ya aikata laifuffuka ya fi a
kirga a duniya. Watakila ba ka taba jin wannan gogan mai suna Henry Earl ba?
Wannan mutumin ya fi kowa shan kamu a duk duniya.
Henry Earl ko kuma kace masa
James Brown ya shiga Tarihin duniya, inda ya zama wanda ya fi kowa shan dauri a
duniya. Sau kusan 1300 Hukuma tana kama wannan mutumi a rayuwar sa. Ko ka taba
jin wani namji a duniya irin sa?
Yanzu haka James Brown ya
kai shekaru 66 a duniya, ya kuma fara shiga gidan yari ne a shekarar 1970,
watau kusan shekaru hamsin da suka wuce. A wancan lokaci Henry Earl yana dan
matashi mai shekaru 20 rak a duniya da haihuwa. An dai saba kama Henry tun
wancan lokacin da laifin maye a cikin Jama’a, daukar makami da dai sauran su.
Henry Earl mutumin Lexington
ne, na Kentucky ta Amurka. Wannan mutumin masifaffen mashayin giya ne dai a
duniya. James Brown dai ya zauna a gidan yari na kwanaki fiye da 6000 a rayuwar
sa ta duniya. A shekarar 2003 yayi kaurin suna a duniya bayan Gidan CNN ta fito
da shi. Watakila Har ma dai ya saba da gidan kaso.
Source: NAIJ.com
Muhammad Malumfashi, Twitter: @Ya_waliyyi
Ikon Allah, to amma shi wannan mutumin ya na kuwa da aure?
ReplyDeleteba ya tunanin halin da iyalan shi da 'ya'yan shi za su shiga ko ma in ce suke ciki?