Monday, October 31, 2016

Ikon Allah: An haifi wani yaro da kafafu hudu



– An ga abin mamaki a Kasar Mozambique yayin da wata mata ta haifi wani jariri mai kafafu barkatai 

 

An haifi wannan jinjiri da kafafu har guda hudu 

 

 

Wannan abu ya faru ne a Yammacin Kasar Mozambique



 
A Kasar Mozambique wani abin al’aji ya faru, inda aka haifi wani jinjiri da kafafu har guda hudu a jikin sa. A cewar Jaridar Magazine Independete ta Kasar, yanzu haka likitoci na kokarin aiki a kan yaron.

Likitocin Asibitin na kokarin ganin sun yi iya bakin kokarin su wajen ceto wannan yaro. Ko da yake dai har yanzu ba a bayyana jinsin jinjirin ko fito da ainihin hoton sa ba, likitoci na shirin yi masa aiki.

Wannan abin mamaki dai ya faru ne a Yankin Manica da ke Yammacin Kasar na Mozambique. Jaridar Magazine Independete-da ake rubutawa da harshen Kasar Portugal ta bayyana cewa mahaifyar wannan yaron ta dauki ciki kana ta haihu lafiya lau ba tare da wata matsala ba.

Sai ga shi an haifi wannan yaro da kafafu guda hudu a jikin sa, sai dai ba yau aka fara samu irin wannan ba. Ko a shekarar nan an haifi wani yaro da kafafu uku a wannan Gari na Manica.


Na fasa: Amarya ta tsere ana tsakiyar daura aure...


– A Jihar Delta Wata Amarya ta ruga a guje yayin da ske shirin daura mata aure

 


Wannan Amarya ta ce ba tayi, ana tsakiyar taro

 


An ga Angon ta a guje yana bin ta a baya, yana ba ta hakuri





A Jihar Delta wani abin mamaki da al’aji ya faru a wannan makon. DailyPost ta rahoto cewa an dakatar da wani daurin aure bayan da Amarya ta sheka a guje ta bar wurin bikin. Wannan Amarya ta ce ita fa sam ta fasa yin auren. 

Bayan ta ruga, can aka hangi Angon ta a baya yana gudu, domin ya shawo kan ta, ya ba ta hakuri. Wannan abu dai ya faru ne a Garin Udu da ke Jihar Delta. Mutane ne dai sun tsaya kallon sarautar Ubangiji, inda suka ga Ango ya bi kan titin Orhunworhun a guje yana neman Amarya ta dawo a daura masu aure.

Ana dai cikin tsakiyar biki, wannan Amarya ta arce a guje ta bar dakin taron, tace fau-fau ta kuma fasa auren. Sai dai har yanzu ba a san menene ya faru, ya jawo hakan ba. Amma dai wannan abu ya ba jama’a mamaki kwarai.


Sunday, October 30, 2016

Shugaba Buhari yayi magana game da Mamman Daura



Alhaji Mamman wa? 




Anyi wata hira da Shugaba Buhari inda aka tambaye sa ko da gaske ba shine ke rike da madafan ikon Gwamnatin nasa ba

 



Shugaba Buhari yace shi kadai ya nemi takara, kuma shi yayi yawon neman kuri’a don haka shine kadai Shugaban Kasa

 



Shugaban Kasar yace wadanda su ke ganin ba a tafi da su ba, can da su gada



Shugaba Buhari yayi wata hira inda aka yi masa wata tambaya game da rade-radin da ake yin a cewa akwai wani Alhaji Mamman Daura wanda shine kamar Shugaban Kasar. Shugaba Buhari yace wannan karya ce ake yi musamman daga Gidan labarai na Sahara Reporters, yace bai san inda suke samo labaran su ba.

Shugaba Buhari yace shi kadai ya nemi takarar Shugabancin Kasar nan, lungu da sako na Najeriya, a jirgi da mota, don haka shi kadai ne Shugaban Kasa ba wani ba. Shugaba Buhari ya kara tambayar ‘Yar Jarida ko shin Mamman wa take nufi da ta kira sunan Alhaji Mamman Daura da ake zargin ya rike madafan ikon Kasar. Yace wannan karyar banza ce.

Shugaba Buhari yace bai yadda da ballewar Biafra daga Kasar ba, sai dai ya kira su da su shigo Jam’iyya a buga siyasa da su. Shugaba Buhari kuma ya bayyana shirin taimakon Yankin da Boko Haram suka yi wa barna.

Shugaban Kasar ya kuma ce a karshe duk wanda yake ganin an ware sa a Gwamnati, wannan matsalar su ce, don kuwa shi bai da wata matsala.

Mutane 6 da suke rike da madafan iko a Najeriya




Ana ta kukan cewa wasu mutane sun rike madafan iko a Gwamnatin Baba Buhari

 

Ko su wanene wadannan mutane da ba a san su ba?

 

Kwanaki dai har sai dai matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta koka a Gidan BBC

 


Kwanakin baya, Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta koka da yadda wasu mutane da ba ayi yakin zabe da su ba suka rike madafan iko a Gwamnatin mai gidan ta a Gidan BBC. Haka ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya taba cewa wasu sun karbe madafan iko daga hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. 

Ko su waye wadannan mutane? NAIJ sun cinko mutane 6 da ake zargin su su ke rike madafan iko a Kasar a halin yanzu.


MAMMAN DAURA
Mamman Daura ya zama tamkar Mataimakin Shugaban Kasa, ko da bai da wani takamamen Ofishi, yana cikin wadanda suke rike da madafan iko a Kasar. Ko a lokacin da Buhari yayi mulkin Soja, da shi aka dama. Shugaba Buhari kawu yake a wurin sa, duk da Mamman ne babba.


ABBA KYARI
Shugaban ma’aikatan Gidan Gwamnati, Abba Kyari. Tsohon dan tafiyar Buhari ne, ya rike makamai da dama, tun zamanin Gawon ake damawa da shi.A da har ana rade-radin an dakatar da shi daga aiki, sai ga shi kwatsam Ranar Jumu'a a Ofis, ashe hutu ya tafi.

BABACHIR DAVID LAWAL
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir yana daya daga cikin wadanda suke rike da madafan iko a Kasar nan, kuma ba ya shakkan hakan. Shugaba Buhari na jin ta bakin sa.


Wasu Ministoci
Wasu daga cikin Ministocin Gwamnatin sun zama masu fada a ji a Gwamnatin Buhari da kuma Jam’iyyar su ta APC. Wadannan Ministoci da suke da ta cewa a Majalisar zartarwar Tarayya kuwa sune Tsohon Gwamnan Legas da na Rivers; Babatunde Raji Fashola daRotimi Amaechi, watau Ministan Sufuri da kuma Ministan Wuta, Muhalli da Ayyuka na Kasar.


ISMA’IL FUNTUA
Ko da yake ba kowa ne ya ma taba jin sunan wannan mutumi ba, amma kamar Mamman Daura yana daga cikin mutanen da suke rike da madafan iko a Kasar nan. Isma’il Funtua, aminin Buhari ne yana kuma da ta cewa a tafiyar Gwamnati; yana cikin masu fadawa Shugaba Buhari wadanda za ya nada a Gwamnatin sa


TY Danjuma
Theophilus Yakubu Danjuma, wanda yana cikin manyan Kasar nan. TY Danjuma mai gidan Shugaba Buhari ne tun a Soja da kuma Gwamnati, har yau kuma yana girmama sa. TY dajuma tsohon Janar ne, yana cikin wanda suka yi wa Shugaba Buhari yakin cin zabe. TY Danjuma yayi sanadiyar nada wasu Ministoci da masu manyan mukamai cikin Gwamnatin Buhari.



Muhammad Malumfashi ya fassara wannan a NAIJ Hausa: https://www.naij.com/author/muhammad-malumfashi.html

Saturday, October 29, 2016

An yi Sallar Jumu'a kala biyu a Masallacin Sultan Bello



Ana rikicin limanci a Masallacin Sultan Bello

 



An tsaida Sallar Jumu’a saboda rikicin limanci a Sultan Bello

 



Rikicin Limanci ya barke a Babban Masallacin nan na Sultan Bello da ke Kaduna

 



‘Yan Sanda sun harba bindiga ana tsakar Sallar Juma’a

 



An yi Sallar Jumu’a kashi biyu a Masallacin

 

 

 

Rikicin Limanci ya barke a Babban Masallacin nan na Sultan Bello da ke Kaduna. Abin har ta kai an katse Sallar Juma’a a Masallacin Jiya. Har dai sai da Jami’an tsaro suka shigo cikin lamarin gudun kar a saba doka.

Wani wanda a gaban sa aka yi komai ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Na’ibin Limamin Masallacin ya gabatar da huduba kamar yadda aka saba, ya tashi ya fara bada Sallah, kwatsam kawai sa aka yi kokari a hana sa jan Sallar a Ra’aka ta farko, daga nan ne Jami’an ‘Yan Sanda suka shiga harbar bindiga da borkonon tsohuwa a cikin masallaci


Bayan Jami’an tsaro sun shiga harbi ne, sai kowa ya tsere daga Masallacin, daga nan kuma mutanen dayan Limamin watau Dr. Khalid suka shiga suka fara nasu Sallar Jumu’ar. Bayan dai sun fara kenan wasu matasa suka shigo Masallacin suka hana su Sallar, don dole suka tashi.

Jami’in ‘Yan Sanda ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar wannan rikici a Babban Masallaci na Sultan Bello. An dai jima ana Rikicin Limanci a Masallacin. Su dai ‘Yan Sanda sun ce rayuka suke karewa ba Liman suka nada ba.


Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...