HUDUBAR JUMA’A DAGA
MIMBARIN ITN-ZARIA
Musulmi a bayan Ramadan-Daga Bakin Imam Dr. Saeed Muhammad Yunus
Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah,
Godiya ta tabbata ga Allah SWT wanda ya halicce mu. Mu na shaida cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah shi
kadai, ba shi da ‘da ko mata ko tamka ko wani abokin tarayya ko mataimaki. Muna
kuma shaida cewa Annabi Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Annabi wanda yake jagora.
Allah ya aiko Annabin sa domin yayi wa’azi na gaskiya
wanda kuma Annabin SAW ya isar da sakon Allah, ya kira mutane, yayi nasiha yayi
hakuri, yayi jihadi har sai da gaskiya ta tabbata. Rayuwar Manzo Allah SAW ta
kasance dukkanta rayuwa ce ta kira ga Allah SWT. Tsira da amincin Allah su tabbata gare sa da Alayen sa da Sahaban sa Mazan jiya da
su ka bada dukiyar su da karfin su da wanda su ka
bi tafarkin Su har tashin kiyama.
Bayan haka, ‘Yan uwa mu ji tsoron Allah a fili da boye
duk inda mu ka kasance:
‘Yan uwa mu ji tsoron Allah kuma ka da mu mutu face mu na musulmi. ‘Yan uwa masu girma ku sani cewa rayuwa ta Musulmin kwarai ta na kula ne da rayuwa irin ta magabata; yadda su ka gabatar da rayuwar su; asali su kuma sun dauko ne daga hoton rayuwar Manzon Allah. Rayuwar Mumuni tana cike ne da da’a ga Allah mai girma. Saboda haka ya ku ‘Yan uwa masu girma a makon da ya gabata mun kasance mu na azumi, mun yi tsayuwar dare sannan mu na ta karatu da zikiri tare da addu’o’i, ana kuma sadaka iri-iri don neman yarda da tsoron azabar Allah. Allah ya karba mana. ‘Yan uwa wata mai girma ya wuce. Shekaru sun ragu, kwanaki sun tafi. Don haka ne Huduba ta ke fada mana cewa kowa ya duba yayi wa kan sa hisabin abin da ya aikata, shin wani tasiri aka samu a cikin wannan wata, ko shin mun yi koyi da abubuwan da ke sa a karbi aiki? Ko kuwa dai an samu akasin haka ne? Shin mun dauki hanyar wadanda su ke kuka yayin da wannan wata ke tafiya? Ko kuwa mun dauki hanyar mutanen da ke murna da wucewar wannan wata? Wadancan Bayin Allah magabata sun kasance kuka su ke yi da zarar wannan wata ya tafi har na watanni 6. Ubangiji ya siffanta irin wadannan Bayi na gari a cikin Suratul Mu’uminuna a cikin Al-Kur’ani. Aisha mai gaskiya ‘yar mai gaskiya RAA ta tambayi Mijin ta Farin Jakadan Allah SAW game da wadannan Bayin Allah, sai Annabi SAW ya fada mata cewa su ne wadanda su kayi sallah da azumi su ka bada sadaka da dukiyar halal amma kuma su na tsoro ko an karba masu. Ya ku Jama’a ku ji tsoron Allah.

Huduba tana fada maku cewa kowa ya duba abin da ya
samu cikin wannan azumi da ya wuce; riba ko asara. Daga cikin abubuwan da ake
gani na cewa Bawa ya dace shi ne ya dage cikin wadannan ayyuka na alheri. Allah
ya sa mu cikin wadannan. Wasu da yawa idan Ramadan ya zo sai ka ga sun riga
Liman zuwa Masallaci, kowa ya tsuguna yana rokon Allah, amma da zarar Ramadan
ya wuce shikenan. Duk wanda ya kasance ya canza daga abin da yake yi lokacin
Ramadan bai karu da komai ba. Allah ka tsare mu. Abin kunya ne kuma bako ga ’Dan Musulmi ya
munana fahimtar sa ga wannan addini da farin jakada Annabi Muhammadu SAW ya
kawo domin rahama da sauki. A ce Musulmi ba shi da wani lokaci na yin ibada sai
illa cikin watan Ramadan kacal. Ayar Kur’ani cikin Suratul Nahli tayi gargadi
daga irin wannan. An tambayi Magabata game da masu ibada kadai a lokacin azumi
cikin Ramadana, sai yace wadannan Mutane ba su san Allah ba sai watan Ramadana.
A wata ruwayar kuma sai aka ce wadannan mutane su ne masu bautar Ramadan. Allah
ka sa mu dace da abin da muka aikata ka amsa mana.
Bangare na biyu na Huduba bayan godiya ga Allah mai gusar
da bakin-ciki ya kuma samar da ni’ima tare da shaidawa bai da abokin tarayya.
Haka kuma Annabi Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Annabi wanda Ubangiji ya aiko ga dukkanin Duniya. Allah ka yi
tsira da shi da Iyalan sa da Sahaban sa. Mu kara godewa Allah bisa ni’iomi da
falala da dama da Yayi mana. Allah ya jero mana falala da dama; wanda daga
Ramadan sai kuma aikin Hajji, haka nan sai ka ji azumi, ka ji kuma Sallar Juma’a
kowane mako. Ubangiji ya zabi wannan al’umma yayi mata wannan kyauta. Allah ka
samu cikin wadanda Ka ke daga darajar su Ka kankare mana zunuban mu.
‘Yan uwa daga cikin abubuwan da ya kamata mu kiyaye kuma mu tsare cikin wannan wata na Shawwal shine azumi guda 6. Kowa yayi kokari saboda Hadisin nan na Imam Muslim wanda yake cewa duk wanda ya azumci watan Ramadan kuma ya bi da kwanaki shidda cikin Watan Shawwal, to kamar ya azumci daukacin shekarar ne. Musulunci saboda sauki ya bada dama ba dole sai anyi wannan azumi a jere ba. Ka da ka yarda a ce Wata ya kare ba ka kammala wannan azumi ba; ka kasance cikin wadanda su ka yi wauta, su kayi asarar wannan garabasa. ‘Dan uwa mai hankali shi ne wanda da zarar ya ji aiki na alheri sai yayi wuf ya auka masa kafin lokaci ya auko masa don kuwa ajali na iya yankewa, rayuwa ta kare masa. Amma kuwa Wawa shi ne wanda yake tunanin yana da saura don kuwa har iyayen sa na nan da rai. Wani ya kan kirga shekarun da kakannin sa su kayi a Duniya. Lallai duk wanda yake cikin wannan dabi’a ba zai karu da komai ba sai nadama a lokacin da ba za tayi amfani ba.
Huduba ta na nasiha ga Samari da cewa su yi hankali
don kuwa rayuwa kadan ce, ajali kuma an yankewa kowa. Haka za ayi ta kirga
numfashi har ranar da za ace babu saura, amma kai ba ka sani ba. ‘Yan uwa mai
ke damun Samarin Musulmi ne yayin da ake ayyukan alheri sai ka ga su na shiga
ta kafirai kuma su na shaye-shaye abubuwan da Musulunci ya haramta wai don
murnar Sallah. ‘Ya ‘yan Musulmi sun a zubar da jini su na barna a Ranakun Idi. Wannan
kaskanci kurum su ka karawa Musulunci. Dama Annabi SAW ya fada cewa a karshen
Duniya wadanda ba su da rabo abin da za su rika yi kenan. Samari su na zubar da
jinane bayan sun sha kayan maye, su na kashe Jam’a ba dalili, su na rusa
gine-ginen da aka yi. Jama’a ku sani cewa Hukuma na da karfi wajen hana wannan
da murya da ta fi karfin kowace wajen dakatar da wannan abu. Mu na godiya game
da matakan da mu ka ji Hukumar za ta dauka ga masu sokawa Jama’a wuka su na
kashe su yayin da ake bikin Sallah. Allah ya karawa Hukuma karfi wajen zakulo
wadannan mutane masu barna. Allah ya kare al’umma daga wannan bala’i, ya zama
mu na tsoro yayin da ake farin ciki. Ina kira ga Iyaye cewa kowa ya duba ya ga
abokan ‘Ya ‘yan sa. Haka Malamai, na san ba abin da za ku iya face fada-aji
kamar yadda nake yi a nan, na dauki mataki irin naku. Ku kiyayi ‘Ya ‘yan ku don
kuwa a gobe Kiyama kowane Uba zai amsa tambaya gaban Allah Madaukaki game da
abin da ‘Dan sa ya aikata. Idan har ba ku hana su ba, wannan abu lallai ya zama
ruwan dare a Arewacin kasar nan. Mu na roko Allah SWT ya karawa Hukuma na
Sojoji, ‘Yan Sanda har na boye gaskiya wajen zakulo wadannan yara.
Daga karshe kuma Huduba tana fadawa Hukumar Alhazai
cewa kudin Hajji yayi yawa. Idan har ba ku san wadanda su ka zabi wannan
Gwamnati ba to talakawa ne. Talakawa za su yi addu’a ta rushe idan ba a canza
tsari ba. Kudin Hajji ace har Miliyan daya da rabi lallai yayi yawa. Talakawa
ne manoma su ka biya kudin Hajji bana. A rage wannan kudi zuwa N500, 000 ko
N800, 000 ko kuma a kyale sa yadda yake bara. Mutane lallai su na cikin wani
hali na kani-ka yi. Mu na kuma kira ga wadanda ke cikin Gwamnati da su yi ta ka
tsan-tsan su san cewa wata rana za a sauke su don wata rana ba Buhari ba ne
Shugaban kasa ko El-Rufai ne Gwamna kuma tarihi zai dauko cewa an tsula kudin
Hajji a lokacin ku. Akwai wasu da ba su so a ci nasara cikin tafiyar nan, amma
ku san ku ka tsaya kuma Talakawa su ka zabe ku. Duk wanda ya san aikin Hajji ya
san cewa wannan kudi yayi yawa. Akwai Hukumar da ke cewa zai biyawa Mahajjata
bukatar su a kudi da lokacin da bai kai na Hukumar kasa ba amma ana ta kokarin
shagube, a ba da dama mana idan ba so ku ke Allah ya rusa Hukumar Alhazan ta
kasa ba. Ku sani cewa lallai Allah yana kallon ku. Allah ya shirye ku ko kuma
ya kawo wadanda za sum aye gurbin ku. Lallai abin ya tsanan ta.
Allah ka dada tsira ga Annabi Muhammadu SAW. Allah ka
tsawaita mana rayuwar mu ka yafe mana. Allah kar ka sa wuyayan mu da na Iyayen
mu su shiga wuta. Allah ka taimaki Musulmi kar ka yi taimako a kan sa. Allah ka
sa mu cika da imani ka ba mu lafiya. Allah ka ba Shugaban kasa lafiya ka
taimaki kasa da shi Allah.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga
Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment