Karon farko: Ka ga wadanda aka gani
tare da Shugaban kasa Buhari jiya a Landan
- Jiya wasu Gwamnonin APC su ka
gana da Shugaba Buhari a Landan
- Shugaban Jam'iyyar APC da wani
Ministan kasar na cikin tawagar
- Tun bayan tafiyar Shugaban kasar
sai jiya aka iya ganin hoton sa
A
Jiya ne wasu Gwamnonin Jam'iyyar APC su ka gana da Shugaban Kasa Muhammadu
Buhari a Birnin Landan.
Wadannan
Gwamnoni sun hada da:
- Malam Nasir El-Rufai
Gwamnan
na Jihar Kaduna kuma na hannun daman Shugaban kasar yana cikin wanda su ka
zauna da shi a jiya.
- Rochas Okorocha
Gwamnan
Jihar Imo kuma Shugaban Gwamnonin APC yana cikin tawagar da ta gana da Shugaba
Buhari.
- Umar Tanko Al-Makura
Har
Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa aka tafi zuwa Landan domin ganin
Shugaba Buhari.
- Yahaya Bello
Haka
kuma Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello na cikin wadanda su ka ziyarci Shugaban
kasa Muhammadu Buhari jiya a Landan.
Sannan
kuma:
- Rotimi Amaechi
Ministan
sufuri na kasar watau Rotimi Amaechi shi na yana cikin wanda su ka gana da
Shugaba Muhammadu Buhari.
- John Oyegun
Shugaban
Jam'iyyar APC John Odigie-Oyegun ma yana cikin tawagar da ta je ta gana da
Shugaban kasar da yake ta faman jinya.
A duk Lokacin da Shugaban kasar ya murmure kuma
Likitocin sa a Ingila su kace ya koma bakin
aiki zai dawo gida.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment