Real Madrid na daf da kafa tarihi
wajen sayan Dan wasa mafi tsada a Duniya
- Real Madrid ta shiga yarjejeniya
da Monaco domin sayen wani Dan wasa
- Dan wasan gaban na Faransa Mbappe
zai ci kusan Dalar Euro Miliyan 180
- Idan ta tabbata matashin Dan
wasan zai zama mafi tsada a kaf Duniya
Real Madrid ta shiga yarjejeniya da Monaco
Muna
samun labari daga Jaridar Marca ta Kasar Sifen cewa Kungiyar Real Madrid ta
shiga yarjejeniya da Kungiyar Monaco domin sayen Dan wasan gaban ta Kylian
Mbappe.
Real
Madrid ta shirya kashe kudi har Euro Miliyan 180 domin kawo wannan matashin Dan
wasa. Idan har cinikin ya tabbata, Dan kwallon zai zama mafi tsada a Duniya
sama da irin su Paul Pogba da aka saya Miliyan 105 a kakar bara.
Matashin
dai yana cikin wadanda ake yi ganin cewa za su addabi Duniya nan gaba kadan.
shiyasa ma dai irin su Kungiyar Chelsea da Manchester City su ka dage wajen
ganin sun saye Dan wasan mai tasowa.
Yanzu
dai an fi ganin Dan wasan gaban na Faransa zai tafi Real Madrid inda zai rika
karbar Dala Miliyan 7 a kowace shekara.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment