Kwakwalwar
wani Dan wasan kwallo ta buga ana cikin wasa
- Kwakwalwar wani babban Dan wasan Ajax tayi raga-raga
- Babban Dan wasan ya samu wannan larura ne a filin wasa
- 'Yan kwallon Duniya su na ta aika sakonnin jinya ga Dan wasan
Kwanaki kun ji labarin
cewa wani Dan wasan Ajax ya kife ana tsakiyar kwallo. Yanzu dai ta tabbata cewa
Kwakwalwar wannan Dan wasan ta samu matsalar da ba zai warke ba.
Kwanan nan mu ka samu
labari cewa kwakwalwar Dan wasa Abdelhak Nouri na Kungiyar Ajax tayi dameji.
Bisa dukkan alamu dai wannan ba karamar lalura bace wanda ba ma wasan kwallon
kafar kadai za ta hana sa ba.
Kungiyar sa ta Ajax da
ke kasar Holand dai wannan abu bai ma ta dadi ba. Haka sauran manyan 'Yan wasan
Duniya sun aika sakon addu'o'in su ta kafafen zamani irin su Tuwita ga wannan
mashahurin Dan wasa da Iyalin sa.
Dan wasan tsakiyar na
Ajax Abdelhak Nouri ya fadi ne bayan an kusa doka Minti 70 da take wasan da ake
karawa ta Kungiyar Werder Bremen na kasar Jamus kwanaki.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment