Sabo Bakin zuwo: Tsohon Gwamnan
Kano da Buhari ya yankewa shekaru 300 a gidan yari
- Sabo Bakin-zuwo yayi Gwamnan
Jihar Kano a shekarar 1983
- Bakin-zuwo ya buge Abubakar Rimi
ya hau kujerar Gwamna
- Sai dai bai je ko ina ba Janar
Buhari yayi juyin mulki a Kasar
Wanene Sabo?
Sabo
Bakin-zuwo yayi Gwamnan Jihar Kano na dan lokaci a shekarar 1983 bayan ya doke abokin
hamayyar sa Gwamna Abubakar Rimi bayan Rimi ya sauya sheka. Asali iyayen Sabo
mutanen Kasar Neja ne su ka tare a Kano.
Kafin zama Gwamna
Kafin
nan Sabo yayi Sanata a shekarar 1979 inda ya tabuka abin kirki a Majalisar.
Sabo ya wakilici Kano ta tsakiya ne a lokacin daga shekarar 1979 zuwa 1983.
Gwamnan Jihar Kano
Sabo
ya zama Gwamna a karkashin Jam'iyyar PRP bayan ya doke Abubakar Rimi. Sabo ya
kawo sauye-sauye a lokacin sa daga ciki har da rusa wasu Masarautu.
Karatun Boko
An
ce Sabo bai taba karatun Boko ba amma dai yace yayi karatun sa ne a gidan
babban Dan siyasar nan Malam Aminu Kano. Bakin-zuwo dai yayi aikin kamfe ta
kafafen rediyo.
Zuwan Janar Buhari zuwa gidan Yari
Janar
Buhari ya kifar da Gwamnatin kasar a karshen shekarar ta 1983. Janar Buhari ya
kama manyan 'Yan siyasar Kano da dama ciki har da Gwamna Sabo. An samu kudi
kusan Dala Miliyan 10 na wannan lokaci a gidan sa. Gwannan yace dai kudin Jihar
Kano ne ya adana a gidan sa. Shugaban kasar Janar Buhari ya yankewa Sabo
Bakin-zuwo da wani Kwamishinan sa shekaru 300 a gidan yari.
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan daga Abiyamo.com ya kuma fara bugawa a NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment