Wani
matashi ya saida motar uban sa araha banza domin ya saye kwayoyi
- Wani yaro ya saida motar uban sa a banza don ya samu sayen kayan marisa
- Wannan matashi ya saida motar sama da Miliyan 7 ne a araha
- A karshe dai duk tsadar motar ta tashi ne a N350,000 kacal
Wani saurayi ya shiga
hannun Hukumar NDLEA. An kama wannan yaro ne
ya saye manyan kwayoyi. Wannan abin asshan ya
faru ne a can Jihar Abiya.
Hukumar NDLEA mai yaki
da fataucin miyagun kwayoyi yayi ram da wani yaro a Garin Umahia a can Jihar
Abiya ya saida manyan motocin Mahaifin sa kirar Jif ta Lexus mai tsadar kudi
Naira Miliyan 7.5 a kan N350, 000.
Wannan saurayi yayi wannan
aiki ne domin kawai ya samu na sayen kwayoyi. Wannan yaro ya zama dai har ba
abin da ba zai iya saidawa ba domin ya samu abin da zai yi shaye-shaye Inji
wani Jami’in Hukumar.
Sai dai akwai na Allah
a ko ina don kun ji wata Ma’aikaciyar Gwamnati a Jihar Kogi ta maida sama
Miliyan 1.78 da aka tura mata a asusun bankin ta bisa kuskure a cikin kwanan
nan.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment