Yusuf
Muhammadu Buhari ya kammala karatu a Turai
- Yusuf dan gidan Shugaba Buhari ya kammala karatu
- ‘Dan Shugaban
kasar ya gama Digirin sa na biyu
- Yusuf ne kadai ‘Dan Shugaba Buhari namiji a Duniya
Mun
samu labari cewa ‘Dan gidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Yusuf ya
kammala karatun sa a Jami’ar Ingila da
ke Turai.
Yusuf
Muhammadu Buhari ya kammala karatun sa na Di-gir-gir kamar yadda wani abokin sa
bayyana a shafin sa na Facebook. Kwanakin baya ne dai wasu ‘Ya ‘yan shugaban
kasar su ka gama karatu a wata Jami’a a kasar Ingila.
Yusuf
ne kadaai ‘Dan Shugaba Buhari namiji a Duniya don kuwa ‘dayan ‘Dan shugaba
Buhari ya rasu. Yusuf na yawan zama a gida Daura kamar yadda mu ka ji kuma
mutum ne mai saukin kai.
Ya kamata Baba Buhari Ya fara Yan Yan shi Su dawo gida suyi karatu.
ReplyDelete