In so samu ne: In kara samun yara
Inji mai 'Ya 'ya 100
- Wani mutumi 'Dan kasar Ghana ya haifi 'ya 'ya fiye da 100
- Amma fa yace so samu ya kara samun wasu ‘ya ‘yan
- Wannan ta’aliki yana da mata har 12 a halin yanzu
Gidan
BBC tayi hira da wani mutumi 'Dan kasar Ghana da ya haifi 'ya 'ya fiye da 100 a
Duniya kuma yace har yanzu bai gaji da samun yaran ba.
Kwanan
nan aka yi bikin al'umma ta Duniya inda wannan mutumi mai suna Kofi Asilenu a
wani Kauye cikin Kasar Ghana mai 'ya 'ya 100 da mata 12 yace shi fa har gobe in
zai samu karin 'ya 'ya yana so.
Wannan
mutumi yace bai da kowa a Duniya na Danuwa don haka ya dage wajen tara 'diya.
Asilenu yace duk da shekarun sa 80 amma har yanzu da karfin sa don haka so ma
yake ‘ya ‘yan na sa su wuce haka.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment