Buri na in samu 'Ya 'ya 7 a rayuwa
inji Ronaldo
- Dan kwallon Duniya Ronaldo yace burin
sa ya samu 'Ya 'ya 7 a rayuwa
- Tauraron Dan wasan yace yana da
bukatar samun 'ya 'ya 3 nan gaba
- Kwanan nan dai Dan wasan ya samu
tagwaye tubarkalla
Mun
samu labari cewa Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana yawan 'ya
'yan da yake so ya haifa. Dan wasan yadda yake goya lamba 7 haka yake so ya
goya 'ya 'ya 7.
Babban
Dan wasan Duniyan yana da 'ya 'ya 3 yanzu wanda babban yake da shekaru 7 sannan kuma ya
samu tagwaye kwanan nan. Ma'ana dai Dan wasan na kasar Portugal na bukatar
karin 'ya 'ya 4 har yanzu.
Yanzu haka dai mun ji cewa Budurwar Cristiano Ronaldo watau G. Rodriguez tana da ciki. Sai dai 'ya 'yan na 'Dan wasan ban da ba a san uwar dukkan su ba, kusan mata dabam su ka haife su. Ronaldo Jr. yana bukatar ayi masa 'yan kannai 6.
Kwanaki dai Dan wasan na Real Madrid din ya samu
jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve daga Kasar Amurka.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment