Mai son Duniya ya rage barci: Dangote ya bayyana sirrin arzikin sa
- Alhaji Aliko Dangote ya bayyana yadda ya
samu arzikin sa
- Bakin Attajirin yace ya zage ne ba dare
ba rana da nema
- Dangote yace a rana bai fi ya
runtsa na dan lokaci kadan ba
Mai
kudin Najeriya da Afrika Aliko Dangote ya bayyana yadda ya samu arzikin sa a
Duniya. Attajirin yace ya zage ne ba dare ba rana wajen nema.
Aliko
Dangote yace a kowace rana ya kan yi aiki har na sa'a 18. Tun karfe 8:30 na
safe Dangote yake shiga Ofis kuma ba zai fito ba sai bayan awa 18. Wannan dai
ya bi jikin sa don kuwa bai fi yayi barci awa uku tak a raba ba.
Dangote
yace ya kan tun karfe 5:00 na asuba bayan yayi sallah sai ya shiga atisaye inda
yake motsa jiki da tafiya ta kilomita 10. Mike Adenuga ya taba ba Dangote
shawara yanzu ya kamata fa ya rika runtsawa don shekaru sun ja.
Duk
Afrika dai babu wanda ya kama hanyar arzikin Dangote wanda ya mallaki sama da
Dala Biliyan 16. Dangote na da ma'aikata akalla 26,000 a wajen harkar noma, abinci,
mai, kayan gini dsr.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment