Ka ji Sanatan da ya fi Dangote arziki amma bai da ko gida a Abuja
- Sanata Kabiru Marafa yayi da'awar
kera Dangote dukiya
- Sanatan yace a wajen sa wadatar
zuciya ita ce Dukiya
- Marafa yace idan kuwa haka ne to
ya girmi Dangote a arziki
Sanata
Kabiru Marafa na Jam'iyyar APC da ke Wakiltar Jihar Zamfara a Majalisar Dattawa
yayi da'awar kera mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote dukiya inda yace shi na
shi mizanin awon dabam.
Babban
Dan Majalisar yace a wajen sa shi wadatar zuciya ita ce arziki amma ba tsabar
kudi ba. Sanatan yace idan kuma wannan ake magana to shi hamshakin attajiri ne
don kuwa yana da wadatar zuci kwarai.
Sanatan
yace har yanzu hayan gida yake yi a Abuja kuma yace kashi 60% cikin 100% na
abin da ya samu hannun mutanen da su ka zabe sa yake komawa. Snatan dai ya nuna
cewa bai da handama ko kadan.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment