Monday, July 10, 2017

Dan wasan Ingila Wayne Rooney ya koma gida




Babban Tauraron Ingila ya bar Kungiyar Manchester United


  • Babban Dan wasan Kungiyar Manchester United  Rooney ya tashi
  • Dan wasa Rooney ya koma Kungiyar sa ta fari Everton
  • Manchester United ta sayo Dan wasa Lukaku daga Everton





Babban Dan wasan nan na kasar Ingila Wayne Rooney ya tashi daga Manchester United inda ya shafe fiye sa shekaru goma yana wasa.

Dan wasa Rooney ya koma Kungiyar da ya baro tun yana Dan shekara 18 Everton inda ya sa hannu kan kwantiragin shekaru 2 ya kuma amince ya rage abin da ya saba karba a Manchester United na albashi.

Wayne Rooney ya ci wa Kungiyar Manchester United kwallaye sama da 250 inda ya doke duk wani tarihi na kulob din. Dan wasa Wayne Rooney ya kuma ci kofi sama da 10 a zaman sa a kulob din.

Haka kuma Manchester United ta sayo Dan wasa Romelu Lukaku daga Everton kan kudi kusan Miliyan  £75. A  Duniyar wasannin dai wani Dan wasan kwallon kafa na Kungiyar Ajax Abdelhak Nouri ya kife ana tsakiyar kwallo kwanan nan.




[NAIJ Hausa] 

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...