Sunday, July 2, 2017

An daura auren Ahmed Musa da Sahibar sa Juliet a Garin su



An yi daurin gargajiyan Ahmed Musa da Juliet a Garin Kuros Ribas


  • An yi daurin gargajiyan Dan wasa Ahmed Musa da Juliet
  • Manyan ‘Yan wasan Najeriya sun halarci wannan taro
  • Daga ciki akwai ‘Dan wasa Raheem Lawal na Super Eagles




 Jiya ‘Yan wasan Super Eagles suka isa Garin Kuros Riba. ‘Yan kwallon sun je Garin ne domin daurin auren Ahmed Musa. Dan wasan na Najeriya ya aure Sahibar sa Juliet a Garin su. 

A jiya 1 ga Wata ne aka yi daurin auren gargajiyan ‘Dan wasan gaban nan na Super Eagles Ahmed Musa da kuma Sahibar sa Juliet Ejue a Garin Ogoja da ke Jihar asalin Kuros Ribas inda matar ta sa ta fito. Idan ba a manta ba Mahaifiyar sa dai ‘Yar Jihar Edo ce.




Manyan ‘Yan wasan Super Eagles irin su Raheem Lawal sun isa har kauyen Mbube domin wannan babban taro. A baya dai an yi bikin auren wanda sai yanzu ne aka na asalin gargajiyar. Ahmed Musa dai ya rabu da Matar sa Jamila kafin yayi wannan aure.

A jiyan ne kuma babban Dan wasan Duniya Messi ya shiga daga ciki. Lionel Messi ya auri sahibar sa mai suna Antonella Rocuzzo wanda su ke tare su na yara.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...