Sabon
salo: Masana sun yi wayar da ke aiki da haske
- Masana sun yi wayar da ke aiki da haske ba ruwan ta da batir
- Idan kana da wannan waya ba ruwan ka da cajin batiri a wuta
- Ana sa rai cigaban ba kuma ya dara haka nan gaba
Masana sun kirkiro
wayar da ba ta aiki da batiri sam abin ta. In dai a irin su Najeriya ne da
lantarki ya zama kayan gabas ai an more kuwa.
Ko da yake a ko ina ma
dai ana kuka wajen yanayin aiki da batiri don haka ne aka kirkiro wannan waya
da ke amfani da haske wajen aiki da kuma karfin sigina wanda ita ce ta farko da
aka taba yi a Duniya wanda ko kadan ba ta aiki da batiri.
Shugaban wadanda su ka
yi wannan nazari da aiki Farfesa Shyam Gollokota da ke Jami'ar Washington na kasar
Amurka yace sun yi tunani ne su ka ga ya dace ayi wani abu game da wannan batu.
Nan gaba da na dai za a kirkiro salular da ke aiki da iska ba mamaki!
[NAIJ Hausa]
Masha Allah, Allah Ya Sa world policy za Su amince wayar ta yaiwa a dukiya har ta Yi Yawa a nan Nigeria. Ameen
ReplyDelete