Monday, July 3, 2017

Abin da ya sa ba za a taba mantawa da Dan Masanin Kano ba



Rasuwar Maitama Yusuf ta bar babban gibi a Najeriya


  • Rasuwar Dan Masanin Kano ya bar gibi a kaf Najeriya
  • Gwamnatin Kano ta bada hutu domin makokin Marigayin
  • Maitama Sule yana cikin Ministocin farko a Najeriya



A kan ce da zarar an yi rasuwa to an rasa mutum, amma idan tsoho ya rasu to tarihin kasa ya fadi. Dan Masanin Kano Ambasada Yusuf Maitama yana cikin wadanda ke rike da tarihi da sirrin Najeriya.

Dan Masanin Kano ya rike mukamai da dama wanda har ya taba zama Minista yana kasa da shekaru 30. Dan Masani mutum ne da ya iya magana kwarai da gaske. Maitama ya taba zama Ambasadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.

Maitama Sule ya taba takarar Shugaban kasa a shekarar 1979 sai dai bai samu ko nasarar lashe zaben fitar da gwani ba wanda Shehu Shagari yayi nasara. Daga baya dai ya zama Ministan Shagari na dan lokaci.

Dan Masani ya taba cewa: Idan har sanin Shugabanci ne da iya jagoranci sai Bahaushe. Sanin kasuwanci kuma sai Inyamuri. Shi kuwa Bayarabe mutum ne da ke gudun tashin hankali a rayuwar sa. Ka ji Maza! Allah ya jikan sa!


            

Muhammad Malumfashi ya fara bugawa wannan a shafin NAIJ.com Hausa

1 comment:

  1. Babba! Babbar kago ta fadi, tarihi ta tafi, maye gurbin Sa, har Abada,saidaimuyi masa fatan gidan Aljannatul firdaus.

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...