Yaki zai tashi tsakanin Kasar
Amurka da Koriya ta Arewa?
- Yaki na nema ya barke tsakanin
Amurka da Kasar Koriya ta Arewa
- Shugaban Amurka yace idan ta kama
sai ya kai wa Koriya hari
- Kwanan nan Koriya ta saki wani
mugun makami mai linzami
Shugaban
Kasar Amurka Donald Trump yace idan ta kama sai ya kai wa Koriya ta Arewa hari
don ya taka masu burki wajen makami mai linzamin da su ke harbawa.
Kwanan
nan Kasar Koriya ta Arewa ta saki wani mugun makami mai linzami wanda ka iya
dura kan Garin Alaska. Amurka tace dole a takawa Koriya burki ko ta karfi da
yaji idan ta kama don ta saba doka bayan da ta saki wani mahaukacin makami mai
linzami.
Amurka
tace za ta fi so a zauna yi sulhu amma fa idan abin ya faskara dole Kasar ta
tashi tsaye. Kwanan nan dai Koriya ta saki makamin nukiliya da zai iya ratsawa
har Kasar Amurka wanda Donald Trump yace ba zai yarda hakan ta faru ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment