Friday, June 30, 2017

Ayyiriri: Yau Dan wasa Lionel Messi zai yi aure



 Yau Dan wasan Duniya Messi zai zama Ango



  • Yau Juma’a ne auren Dan wasan Barcelona Lionel Messi
  • Tuni har Jama’a sun fara cika kauyen Dan wasan a Argentina
  • Messi ya gayyaci tsohon Dan wasan Real Madrid Di-Maria



A yau ne babban Dan wasan Duniya Messi zai shiga daga ciki. Lionel Messi zai auri sahibar sa mai suna Antonella Rocuzzo. Tauraron Dan Messi ya dade tare da wannan Budurwar ta sa tun su na kananan yara. 

A yau ne Dan wasa Lionel Messi na Barcelona zai zama Ango a Birnin Rosario da ke Kasar Argentina. Dan wasa Lionel Messi zai auri Budurwar sa da su kayi shekara da shekaru tare tun su na kanana Antonella Roccuzzo.




Tuni dai har Birnin Rosario ya cika makil wurin daurin auren da ba a taba yin irin sa ba cikin shekaru. Abokan wasan ‘Dan kwallon na Barcelona da sauran su sun fara hallara a jirgi. Messi ya gayyaci ‘Dan kasar sa kuma tsohon Dan wasan Real Madrid Angel Di-Maria.

Haka kuma kun ji cewa babban Dan wasan nan na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve.




[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...