Mutane sun yi wa Gwamna El-Rufai kaca-kaca
bayan ya soki su Sardauna
- Mutane dai ba su ji dadin kalaman
Gwamna El-Rufai ba
- Nasir El-Rufai ya soki Marigayi
Sardauna da su Zik
- Tuni dai wasu su kace ba su cikin
wannan magana
Mun
fahimci cewa kalaman Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai bai yi wa jama'a dadi
ba na sukar manyan kasar nan da yayi kwanan nan a wani bidiyo da ya
bayyana.
Gwamnan
Malam Nasir El-Rufai yace su Sardauna sun yi sakaci wajen mulkin da suka yi. Yace
Marigayi Sardauna Ahmadu Bello ba su yi kokari wajen gina kasar ba sai su ka
buge da tada bangarorin su don manufar su ta siyasa.
Wasu
dai sun ce wannan katobarar ba yau Gwamnan ya fara yin irin ta ba kuma ba su a
cikin wannan suka. Wasu dai dama sun ce ai tun farko su Sardauna ba marasa yin
laifi bane sai dai alherin su ya dara muguntar su.
El-rufai
yace ko ba a fada ba manyan na wancan lokacin sun yi kuskure don kawai su ci ma burin su. Wani
yace shi kan shi Gwamnan da bazar su yake rawa don haka ya ji da dai aikin gaban
sa na Shugabancin Jihar Kaduna.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment