Friday, July 14, 2017

Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N



TAKAMA DA MUSULUNCI



Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria

Daga Bakin Sheikh S.S Abubakar


Bayan shaidawa da gaskiya cewa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah mai girma, shi kadai yake bai da abokin Tarayya. Godiya da yabo sun tabbata a gare Sa, Shine mai iko kan komai. Muna shaidawa cewa lallai Shugaban mu Annabi Muhammadu SAW Bawan Allah ne kuma Manzon sa.


Bayan haka:
Duk wanda yake da lafiyayyen hankali to yana da abin gadara a rayuwa. Amma fa babban abin gadara shine addinin Musulunci wanda Allah ya yarda kuma ya zaba don shi ne mafificin ni’ima da mutum zai samu a cikin rayuwar sa kamar yadda yake fada a Ranar da aka kammala wannan addini. Allah SWT Yace ya cika n’ima a kan mu kuma ya zaba mana Musulunci ya zama addinin mu. Saboda haka Musulmi na gaskiya a ko yaushe yana takama ne da gadara da wannan ni’ima tare da aiki a lokutan sa ga wannan addini.

Bayin Allah wannan takama ba magana ce ta fatar baki ba, aiki ne tukuru in har mutum yana takama da wannan addini. Sai mutum ya dage ya mike yayi aiki tukuru don cin burin wannan addini na samun yardar Allah ta bin shiriyar Manzon Sa SAW a cikin dukkan wani motsi a rayuwa.

Samun yardar Allah Mai girma kan kasance ta hanyar kadaita Sa na dagewa da tsayawa kan Tauhidi da bin hukuncin Allah da nisantar abin da Ya hana. A yayin yin hakan dole mutum yayi kokarin tafiya tare da Iyalan sa ba wai shi kadai ba saboda wannan maganar ceto ne daga wuta zuwa Rahama. Allah SWT yayi umarni a Qur’ani cewa Ku tseratar da kawunan ku da Iyalan ku daga wuta wanda makamashin ta Mutane…Dole ne wannan ya ginu a bisa Imani da aiki na kwarai. Allah Madakaki yana cewa Wadanda su ka yi Imani da kuma aiki na gari za su samu Aljanna. Kuma dama Allah SWT yace duk wanda aka tsirar daga wuta zuwa aljanna, hakika ya rabota! Manufar wannan rayuwa dai ita ce bautawa Allah gwargwado kuma bissa yadda ya dace.

Babu wani dalili na gadara da wannan Addini matukar ba ayi istikama kan shari’ar Allah ba. Kuma wannan istikama ita ce bin tafarkin Allah mikakkiya kamar yadda duk Musulmi ke roko a cikin kowace Sallah. A kan wannan dandamali da ke tsakanin umarni da hani Musulmi na kwarai yake tafiya. Amma fa irin wannan tafarki na bukatar abokan tafiya don haka sai Musulmi ya san irin abokan tafiyar na sa. Allah SWT ya koyar da mu cewa mu nemi tafarkin da ba na wadanda aka yi fushi da su ko batattu ba!

A yayin da ake wannan tafiya kullum Musulmi dubawa zai yi ko su wanene abokan tafiyar sa kuma dole su zama masu imani da Allah kuma wadanda su ka tsaya cak da bauta bisa shiryar Manzo SAW tare da ado da halaye irin na Musulunci. A cikin wannan tafiya ta neman dacewar Allah SWT to Musulmi ya san irin mutanen da zai tafi tare da su. Mutanen na ba na kirki ba, sun san Mutanen su; Barawo ya san irin mutanen sa idan har satar za ayi, haka ‘dan fashi da duk wani mai barna. Ta ya mai imani da shiriya ya zama bai san Abokan tafiyar sa ba? Ya kamata Mai Imani idan har ka gan sa tare da Mutanen banza to sai dai larura, kullum yana so ya zama tare da masu gaskiya a matsayin majibinta. Allah yana cewa a Qur’ani mai girma Muminai maza da Mata, sashen su na tare da sashe. Haka kuma Kafirai su ma sashen su na tare da sashe, har sai sun rasa na su, za su dauki Mumuni. Munafukai kuwa Allah yace sashen su daga sashe yake gaba daya. Haka wannan ya zo game da Azzalumai yayin da Allah SWT yake Gatan masu Imani.

Jama’a kowa yana takama ne da abokan tafiyar sa. A duk wani al’amari sai mutum ya nemi abokan tafiyar san a kwarai; Daidai ga noma, Mutum kan nemi masu gaskiya ne da imani irin sa a matsayin abokan tafiya, ba a zuwa a dauko maha’inta marasa gaskiya wajen tafiya. Dukkan mai imani ya san abokan tafiyar sa. Saboda haka Bayin Allah ku tsaya wajen tsare addini; ka da ayi rauni ko bakin ciki wajen wannan jarrabawa.

Allah Madaukakin Sarki game da mai takama da addini sa yace: ‘Wa ya fi kyawun magana irin wanda yayi kira zuwa ga Allah yace kuma a tsaya a yi aiki na gari, a karshe kuma yace ina cikin Musulmi!’ Babu wanda ya fi wanda yayi wannan kirari kyawun magana. Jama’a ka da mu raina addinin mu wanda yayi mana tanadin rayuwa mai kyau a nan Duniya da kuma Lahira. Idan mun shiga baki ciki sai mu koma mu duba inda mu kayi sakaci wanda duk wannan amsa tana cikin addinin nan na mu. Lallai mu na cikin gadara da wannan addini mai albarka kuma mu san abokan tafiyar mu sannan ka da mu bari don rashin hangen nesa mu rungumi abokan tafiya na banza na daga kafirai da sauran masu fasadi.

Allah ya bamu ikon fahimtar AlKurani mai Girma da aiki da shi. Allah ya tserar da ni da k duka daga azaba mai radadi ya shiga da mu Aljanna. Allah ka dada tsira ga Annabi Muhammad SAW da iyalan sa da Halifofin sa, da sauran wadanda suka bi su da kyautatawa. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmai ka buwayar da Musulmai da wannan addini na ka. Allah ka sa sahun Musulmi ya zama guda ka kuma raya wannan kasa ta mu ka kare mu. Allah ka sa albarka bisa abubuwan da ka azurta mu da su. Allah ka warkar da marasa lafiya musamman Shugaban wannan kasa ka kuma jikan wadanda su ka rasu.  Allah ka ba mu zama lafiya kayi mana maganin Azzalumai da Fajirai ka tabbatar  mana da alheri Duniya da Lahira.

-Mallam Salihu S. Abubakar, Masallacin Islamic Trust of Nigeria, ITN, Zaria.




Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria

Twitter: @Ya_waliyyi

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...