Kungiyar Izala: kafuwar ta zuwa
yanzu
- Shekaru kusan 40 da su ka wuce
aka kafa Kungiyar Izala
- Sheikh Ismail Idris Zakariya ne
yayi wannan aiki
- A lokacin Malamin yana ganin cewa
bidi'a tayi yawa a Najeriya
A
shekarar 1978 ne aka kafa Kungiyar Kungiyar Jama'atul Izalatul bidi'a wa
iqamatus Sunnah domin yaki da bidi'a (watau kagaggun al'amura cikin adddini) da
kuma jaddada Sunnar Manzon Allah SAW a maimakon aiki na-gada da na-gani-ana-yi.
Wani
Kyaftin din Soja ne mai suna Sheikh Ismail Idris Zakariya Dalibi na Sheikh
Abubakar Mahmud Gumi wanda ya rika koyar da Jama'a riko da Hadisan Manzon Allah
wanda aka ga kamar ya ci karo da koyarwar Malaman Darika na Sufaye na matukar biyayya da da'a.
Tun
a gidan Soja aka rika rikici da wannan matashi Ismail Idris wanda har aka kai
ya bar gidan Soja ya kafa wannan Kungiya da niyyar yakar bidi'o'i irin wanda
Shehu Usman Danfodio ya yaka shekarun baya irin su taron suna, amfani da laya,
da aiki da malaman duba na tsibbu.
Malaman
Darika dai sun dauki wannan a matsayin fito na fito don haka su ka tashi da
Almajiran su haikan wajen maida martani yayin da ake cewa wasu daga cikin su ma
dai ba Musulmai bane gaba daya.
Kungiyar
dai ta gamu da rikicin siyasa wanda har ya kai ga rabuwar wurin ibada. Kawo
yanzu dai Izala tana cikin manyan Kungiyoyin da ke da ta cewa a harkar
Musulunci da kuma yi wa addini hidima.
Masha Allah. Allah Ya saka da alkhairi. Allah Ya Sa mu dace.
ReplyDeleteAmin ya Allah
Delete