Wata
Shari'ar sai a Lahira: Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana abin da ya faru a
Mambilla
- Shugaban Gundumar Soji yace kusan
da gan-gan aka kashe Fulani a Mambilla
- Janar din yace da wuya ace babu
hannun Hukuma da Jami’ai a barnar
- Sojan yace
wadanda su ka yi wannan aiki sun fi Boko Haram barna
Da laifin Shugabanni a rikicin Taraba-Sojin Najeriya
Shugaban Soji na Yankin Jos yace kisan kare dangi
aka yi wa Fulani. Har mata masu ciki da kananan yara da shanu ba a
bari ba. Bincike dai ya nuna cewa ba mamaki Hukuma na da
laifi a ta’asar.
Bincike kamar yadda Shugaban Gundumar Sojin Najeriya
na Runduna ta uku Birgediya Benjamin
Ohanato ya nuna kusan kisan kare dangi aka yi wa Fulani a Garin Mambilla. Abin
dai har mata masu ciki da kananan yara nmasu shekaru 2 da shanu ba a kyale ba.
Janar din yake cewa da wuya a yarda babu hannu ko
sakacin Hukumar Jihar tun daga mataki na sama har kasa don ba ayi komai ba
lokacin da barnar ta barke. Asali ma dai har lokacin da Soji su ka zo ana kona
kauyukan Fulani. Sojan yayi tir da wannan yace har gara Boko Haram.
Kun ji cewa an kona gidaje da dama na Fulani a
Mambila da ke Garin Sardauna. Mutane da yawa su ka rasa ran su inda wasu su ka
samu rauni na inna-naha bayan sun tsere har ta kai wasu sun bar kasar zuwa
Kamaru.
[NAIJ Hausa]
Haqikah buri yayi kama da mutum! Gwamnati ya kamata ta dau tsautsaurar mataki tare da gudanar da cikakken bincike dangane da wagga al'amari.
ReplyDelete