Tuesday, July 4, 2017

Sanatoci sun yi kokarin nada Saraki Shugaban kasa


Daga fitar Osinbajo wajen Najeriya Sanatoci sun yi kokarin nada Saraki rikon kwarya


  • Sanatocin Najeriya sun yi wani yunkuri a harkar siyasar kasar dazu haka
  • An dai yi kokari a nada Bukola Saraki a matsayin Mukaddashin Shugaban
  • Mukaddashin Shugaban kasar Farfesa Osinbajo yayi tafiya wajen kasar ya dawo



Daga fitar Osinbajo wajen Najeriya Sanatoci sun yi kokarin nada Saraki Shugaban kasa na rikon kwarya dazu. Wasu Sanatoci ne su ka kawo wannan kuduri sai dai tuni Saraki yayi watsi da maganar.

Wani Sanatan Jihar Abiya Eyinanya Abaribe ya fara kawo magana a Majalisa cewa babu Shugaban kasa a Najeriya yanzu haka ganin cewa Mukaddashin Shugaban kasar yayi tafiya zuwa kasar waje domin taron AU na Afrika.

Tuni dai Sanata Kabiru Marafa wanda a da ba ya ga maciji da Bukola Saraki yace ai sai a nada Shugaban Majalisar Dattawan kasar wanda shi ne na 3 a matsayi ya dare kujerar kafin dawowar Shugabannin kasar.

Kwanan ne dama aka ga fasocin Bukola Saraki na takarar Shugaban kasa a Garin Ilorin. Kuma tuni dai Mukaddashin Shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya dawo daga tafiyar da yayi.






[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...