Tuesday, July 4, 2017

Allahu akbar: An bizne ‘Dan Masanin Kano Maitama Sule



Rayuwa kenan: Jama’a sun taru wajen rufe Marigayi Dan Masanin Kano



  • Gwamnan Kano ya jagoranci jama’a wajen birne Marigayi Maitama Sule
  • Shugaban Majalisa Bukola Saraki yana cikin wadanda suka halarci sallar
  • Sauran manyan Gwamnoni da mutanen Kasa sun yi Dattijon Sallah




A jiya ne Dan Masanin Kano ya cika a wani Asibitin kasar Masar. Manyan Kasa dai sun halarci sallar da aka yi masa.  Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Ganduje ya jagoranci jama’a wajen birne tsohon Ministan.

Sauran Gwamnonin Jihohin Jigawa, Bauchi da Sokoto, dsr sun halarci sallar. Haka kuma Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki yana cikin wadanda suka halarci sallar. Sauran Ministocin kasar irin su Hadi Sirika da Kayode Fayemi sun halarci Jana’izar.


Gwamnatin Tarayya ta aiko wakilai karkashin Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati Abba Kyari. A jiya Shugaba Buhari ya aiko takarda ta musamman inda yake takaicin rashin Maitama Yusuf yace an yi rashi.

Babban Jigo a Jam’iyyar APC Bola Tinubu yace ba shakka an rasa wadanda su ka rage cikin iyayen kasar da ake da su. Dan Masanin Kano mutum ne mai baiwar magana kuma mai son kasar nan da gaskiya.






[NAIJ Hausa]

1 comment:

  1. Allah Ya gafarta masa, mu kuma Allah Ya Sa mu cika da kyau da imani.

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...