Rasuwar Maitama Yusuf ta bar babban
gibi a Najeriya
- Rasuwar Dan Masanin Kano ya bar
gibi a kaf Najeriya
- Gwamnatin Kano ta bada hutu domin
makokin Marigayin
- Maitama Sule
yana cikin Ministocin farko a Najeriya
A kan ce da zarar an yi rasuwa to an rasa mutum,
amma idan tsoho ya rasu to tarihin kasa ya fadi. Dan Masanin Kano Ambasada Yusuf
Maitama yana cikin wadanda ke rike da tarihi da sirrin Najeriya.
Dan Masanin Kano ya rike mukamai da dama wanda har
ya taba zama Minista yana kasa da shekaru 30. Dan Masani mutum ne da ya iya
magana kwarai da gaske. Maitama ya taba zama Ambasadan Najeriya a Majalisar
Dinkin Duniya.
Maitama Sule ya taba takarar Shugaban kasa a
shekarar 1979 sai dai bai samu ko nasarar lashe zaben fitar da gwani ba wanda
Shehu Shagari yayi nasara. Daga baya dai ya zama Ministan Shagari na dan
lokaci.
Dan Masani ya taba cewa: Idan har sanin Shugabanci ne da iya jagoranci sai Bahaushe. Sanin
kasuwanci kuma sai Inyamuri. Shi kuwa Bayarabe mutum ne da ke gudun tashin
hankali a rayuwar sa. Ka ji Maza! Allah ya jikan sa!
Muhammad Malumfashi ya fara bugawa wannan a shafin NAIJ.com Hausa
Babba! Babbar kago ta fadi, tarihi ta tafi, maye gurbin Sa, har Abada,saidaimuyi masa fatan gidan Aljannatul firdaus.
ReplyDelete