Sunday, July 30, 2017

Tsohon Dan wasan Real Madrid James ya saki matar sa


Bayan ya bar Madrid Dan wasa James ya bar mai dakin sa


James Rodriguez ya saki matar sa da su ka dade tare


Rodriguez ya rabu da Daniela Ospina bayan shekaru 6 tare


Bayan ya bar Madrid Dan wasa James ya bar mai dakin sa





Mun ji cewa bayan ya bar kulob din Real Madrid Dan wasa James Rodriguez ya rabu da mai dakin sa Daniela Ospina bayan sun yi shekaru 6 tare su na zaman aure.

Dan wasa Rodriguez mai shekaru 26 ya rabu da uwar Diyar sa bisa wasu zargi cikin auren na su. Daniela Ospina 'yar uwa ce wurin dan wasan Arsenal Ospina mai tsaron raga. A watan nan ne dai Dan wasan ya koma Kasar Jamus da kwallo.

Tuni ma dai har an saida daya daga cikin gidajen na su kuma Ospina ke rike da Diyar su Salome mai shekaru 4 da wani gidan su na Amurka.


[NAIJ HAUSA] 

Koriya ta kara sakin wani mahaukacin nukiliya


Kasar Koriya ta Arewa ta kara harba wani mugun makami mai linzami


 - Kasar Koriya ta Arewa ta yi gaba wajen harkar nukiliya


- Kwanan nan Kasar ta kara harba wani makamin


- Wannan ne karo na biyu da kasar ta harba nukiliya






Mun samu labari cewa Kasar Koriya ta Arewa ta yi gaba wajen harkar nukiliya don kuwa Kwanan nan Kasar ta kara sakin wani mugun makamin.

Ku na sane cewa wannan ne karo na biyu da kasar ta harba nukiliya cikin 'yan kwanakin nan domin wani gwajin da ta ke yi. Makamin wannan karon ma dai ya fi wanda aka saki a baya. Kwanaki kasar ta saki irin wannan makami da zai iya barin Nahiya zuwa wata Nahiyar.




BBC ta rahoto cewa wannan makami ya dade yana yawo kafin ya fada cikin ruwa a wani Gari cikin Kasar Japan. Duk da dai takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke dorawa Kasar ta Koriya ta Kudu ba ta tsaya wajen harkar kera makamin ba.

Kwankin baya Kasar Koriya ta Arewa ta saki wani mugun makami mai linzami wanda ka iya dura kan Garin Alaska. Amurka tace dole a takawa Koriya burki ko ta karfi da yaji idan ta kama don ta saba doka bayan da ta saki wani mahaukacin makami mai linzami.



[NAIJ Hausa]

Saturday, July 29, 2017

Yadda nake goya lamba 7 haka nake son goya 'ya 'ya 7



Buri na in samu 'Ya 'ya 7 a rayuwa inji Ronaldo


 - Dan kwallon Duniya Ronaldo yace burin sa ya samu 'Ya 'ya 7 a rayuwa  


- Tauraron Dan wasan yace yana da bukatar samun 'ya 'ya 3 nan gaba


- Kwanan nan dai Dan wasan ya samu tagwaye tubarkalla



Mun samu labari cewa Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bayyana yawan 'ya 'yan da yake so ya haifa. Dan wasan yadda yake goya lamba 7 haka yake so ya goya 'ya 'ya 7.

Babban Dan wasan Duniyan yana da 'ya 'ya 3 yanzu wanda babban yake da shekaru 7 sannan kuma ya samu tagwaye kwanan nan. Ma'ana dai Dan wasan na kasar Portugal na bukatar karin 'ya 'ya 4 har yanzu.




Yanzu haka dai mun ji cewa Budurwar Cristiano Ronaldo watau G. Rodriguez tana da ciki. Sai dai 'ya 'yan na 'Dan wasan ban da ba a san uwar dukkan su ba, kusan mata dabam su ka haife su. Ronaldo Jr. yana bukatar ayi masa 'yan kannai 6.

Kwanaki dai Dan wasan na Real Madrid din ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve daga Kasar Amurka.


[NAIJ Hausa]

Ko ka san barcin awa nawa Dangote yake yi?


Mai son Duniya ya rage barci: Dangote ya bayyana sirrin arzikin sa


  • Alhaji Aliko Dangote ya bayyana yadda ya samu arzikin sa
  • Bakin Attajirin yace ya zage ne ba dare ba rana da nema
  • Dangote yace a rana bai fi ya runtsa na dan lokaci kadan ba


Mai kudin Najeriya da Afrika Aliko Dangote ya bayyana yadda ya samu arzikin sa a Duniya. Attajirin yace ya zage ne ba dare ba rana wajen nema.

Aliko Dangote yace a kowace rana ya kan yi aiki har na sa'a 18. Tun karfe 8:30 na safe Dangote yake shiga Ofis kuma ba zai fito ba sai bayan awa 18. Wannan dai ya bi jikin sa don kuwa bai fi yayi barci awa uku tak a raba ba.

Dangote yace ya kan tun karfe 5:00 na asuba bayan yayi sallah sai ya shiga atisaye inda yake motsa jiki da tafiya ta kilomita 10. Mike Adenuga ya taba ba Dangote shawara yanzu ya kamata fa ya rika runtsawa don shekaru sun ja.

Duk Afrika dai babu wanda ya kama hanyar arzikin Dangote wanda ya mallaki sama da Dala Biliyan 16. Dangote na da ma'aikata akalla 26,000 a wajen harkar noma, abinci, mai, kayan gini dsr.


[NAIJ Hausa]

Thursday, July 27, 2017

Wani Attajiri ya buge Bill Gates daga mai kudin Duniya


Mai laya kiyayi mai zamani: An doke Bill Gates; amma zuwa yaushe?


  • Attajiri Bill Gates shi ya fi kowa kudi a Duniya na dogon lokaci
  • Yanzu an samu wani Attajiri ya sha gaban Mista Bill Gates
  • Jeff Bezos ya kera Bill Gates da kusan Dala rabin Biliyan


Mun samu rahoto cewa an samu wani babban Attajiri mai suna Jeff Bezos wanda ya sha gaban Mista Bill Gates cikin sahun masu kudin Duniya kwanan nan.

Bezos a yanzu maganar da ake yi ya ba Dala Biliyan $90.6 baya. A wancan karo mun samu rahoto cewa Bill Gates ya mallaki sama da Dala Biliyan 86. Wannan na nufin cewa Jeff Bezos ya kera Bill Gates da kusan Dala miliyan 500.



Jeff Bezos

Jeff Bezos ne wanda yake da Kamfanin nan na Amazon kuma tun shekarar 1998 ya shigo Duniya. Shi dai Bll Gates ya kashe sama da Dala Biliyan 3 wajen taimakawa yara da sauran Jama’a a shekarar nan.

Daga bara arzikin Bill Gates ma dai karuwa yayi daga Dala Biliyan 75 zuwa Dala Biliyan 86 a bana. Mista Bill Gates shi yake da Kamfanin Microsoft. Haka kwanakin baya mai kudin kasar Sifen Amancia Ortega ya doke Bill Gates na dan lokaci.




[FORBES]

Wednesday, July 26, 2017

Real Madrid na shirin sayen wani Dan wasan Dala Miliyan 180


Real Madrid na daf da kafa tarihi wajen sayan Dan wasa mafi tsada a Duniya

  • Real Madrid ta shiga yarjejeniya da Monaco domin sayen wani Dan wasa
  • Dan wasan gaban na Faransa Mbappe zai ci kusan Dalar Euro Miliyan 180
  • Idan ta tabbata matashin Dan wasan zai zama mafi tsada a kaf Duniya



Real Madrid ta shiga yarjejeniya da Monaco


Muna samun labari daga Jaridar Marca ta Kasar Sifen cewa Kungiyar Real Madrid ta shiga yarjejeniya da Kungiyar Monaco domin sayen Dan wasan gaban ta Kylian Mbappe.

Real Madrid ta shirya kashe kudi har Euro Miliyan 180 domin kawo wannan matashin Dan wasa. Idan har cinikin ya tabbata, Dan kwallon zai zama mafi tsada a Duniya sama da irin su Paul Pogba da aka saya Miliyan 105 a kakar bara.

Matashin dai yana cikin wadanda ake yi ganin cewa za su addabi Duniya nan gaba kadan. shiyasa ma dai irin su Kungiyar Chelsea da Manchester City su ka dage wajen ganin sun saye Dan wasan mai tasowa. 

Yanzu dai an fi ganin Dan wasan gaban na Faransa zai tafi Real Madrid inda zai rika karbar Dala Miliyan 7 a kowace shekara.


[NAIJ Hausa]

Tuesday, July 25, 2017

Ka taba jin labarin wani Gwamna da Buhari ya daure na shekara 300?


Sabo Bakin zuwo: Tsohon Gwamnan Kano da Buhari ya yankewa shekaru 300 a gidan yari


 

  • Sabo Bakin-zuwo yayi Gwamnan Jihar Kano a shekarar 1983
  • Bakin-zuwo ya buge Abubakar Rimi ya hau kujerar Gwamna
  • Sai dai bai je ko ina ba Janar Buhari yayi juyin mulki a Kasar


Wanene Sabo?
Sabo Bakin-zuwo yayi Gwamnan Jihar Kano na dan lokaci a shekarar 1983 bayan ya doke abokin hamayyar sa Gwamna Abubakar Rimi bayan Rimi ya sauya sheka. Asali iyayen Sabo mutanen Kasar Neja ne su ka tare a Kano.

Kafin zama Gwamna
Kafin nan Sabo yayi Sanata a shekarar 1979 inda ya tabuka abin kirki a Majalisar. Sabo ya wakilici Kano ta tsakiya ne a lokacin daga shekarar 1979 zuwa 1983.

Gwamnan Jihar Kano
Sabo ya zama Gwamna a karkashin Jam'iyyar PRP bayan ya doke Abubakar Rimi. Sabo ya kawo sauye-sauye a lokacin sa daga ciki har da rusa wasu Masarautu.

Karatun Boko
An ce Sabo bai taba karatun Boko ba amma dai yace yayi karatun sa ne a gidan babban Dan siyasar nan Malam Aminu Kano. Bakin-zuwo dai yayi aikin kamfe ta kafafen rediyo.

Zuwan Janar Buhari zuwa gidan Yari

Janar Buhari ya kifar da Gwamnatin kasar a karshen shekarar ta 1983. Janar Buhari ya kama manyan 'Yan siyasar Kano da dama ciki har da Gwamna Sabo. An samu kudi kusan Dala Miliyan 10 na wannan lokaci a gidan sa. Gwannan yace dai kudin Jihar Kano ne ya adana a gidan sa. Shugaban kasar Janar Buhari ya yankewa Sabo Bakin-zuwo da wani Kwamishinan sa shekaru 300 a gidan yari.



Muhammad Malumfashi ya  fassara wannan daga Abiyamo.com ya kuma fara bugawa a NAIJ Hausa

Monday, July 24, 2017

Gwamnoni 4 da su kai wa Buhari ziyara jiya a Landan



Karon farko: Ka ga wadanda aka gani tare da Shugaban kasa Buhari jiya a Landan

 

  • Jiya wasu Gwamnonin APC su ka gana da Shugaba Buhari a Landan
  • Shugaban Jam'iyyar APC da wani Ministan kasar na cikin tawagar
  • Tun bayan tafiyar Shugaban kasar sai jiya aka iya ganin hoton sa


A Jiya ne wasu Gwamnonin Jam'iyyar APC su ka gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Birnin Landan.

Wadannan Gwamnoni sun hada da:

  1. Malam Nasir El-Rufai
Gwamnan na Jihar Kaduna kuma na hannun daman Shugaban kasar yana cikin wanda su ka zauna da shi a jiya.

  1. Rochas Okorocha
Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban Gwamnonin APC yana cikin tawagar da ta gana da Shugaba Buhari.

  1. Umar Tanko Al-Makura
Har Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa aka tafi zuwa Landan domin ganin Shugaba Buhari.





  1. Yahaya Bello
Haka kuma Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello na cikin wadanda su ka ziyarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya a Landan.

Sannan kuma:

  1. Rotimi Amaechi
Ministan sufuri na kasar watau Rotimi Amaechi shi na yana cikin wanda su ka gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

  1. John Oyegun
Shugaban Jam'iyyar APC John Odigie-Oyegun ma yana cikin tawagar da ta je ta gana da Shugaban kasar da yake ta faman jinya.


A duk Lokacin da Shugaban kasar ya murmure kuma Likitocin sa a Ingila su kace ya koma bakin
aiki zai dawo gida. 


[NAIJ Hausa]

Sunday, July 23, 2017

Wani shu'umi a wata kasa yace shi ma Annabi ne



Wani mutumi yayi da'awar Annabta a Kasar Sudan



  • Wani mutumi yace shi Annabi ne kuma ana yi masa wahayi
  • Wannan mutumi ya fito ne daga Yankin Darfur ta kasar Sudan
  • Har da ma wata sura yace an sauke masa ga mutanen sa



Wani mutumi mai suna Abdulwahid Muhammad Nur a can kasar Sudan yace wai shi ma Annabin Allah ne kuma Ubangiji ya turo sa ga mutanen sa.

Wannan 'Dan banza yace ana yi masa wahayi kamar dai Annabawan Allah kuma tuni har an sauko masa da wata Sura mai suna Sural Darfur watau ta mutanen Garin Darfur da ke Kasar Sudan.

A surar dai kamar yadda mu ka ji yana karanta ta, an ambaci mutanen Darfur da ma na Nahiyar Afrika da kuma shi karen kan sa wannan mutumi a ayoyin ta. 

Wannan mutumi Abdulwahid Muhammad yace Ubangiji ne ya aiko sa domin ya gargadi Jama'a daga azaba.



[NAIJ Hausa]

An yi wa El-Rufai kaca-kaca bayan ya soki su Sardauna


Mutane sun yi wa Gwamna El-Rufai kaca-kaca bayan ya soki su Sardauna


  • Mutane dai ba su ji dadin kalaman Gwamna El-Rufai ba
  • Nasir El-Rufai ya soki Marigayi Sardauna da su Zik
  • Tuni dai wasu su kace ba su cikin wannan magana





Mun fahimci cewa kalaman Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai bai yi wa jama'a dadi ba na sukar manyan kasar nan da yayi kwanan nan a wani bidiyo da ya bayyana. 

Gwamnan Malam Nasir El-Rufai yace su Sardauna sun yi sakaci wajen mulkin da suka yi. Yace Marigayi Sardauna Ahmadu Bello ba su yi kokari wajen gina kasar ba sai su ka buge da tada bangarorin su don manufar su ta siyasa.

Wasu dai sun ce wannan katobarar ba yau Gwamnan ya fara yin irin ta ba kuma ba su a cikin wannan suka. Wasu dai dama sun ce ai tun farko su Sardauna ba marasa yin laifi bane sai dai alherin su ya dara muguntar su.

El-rufai yace ko ba a fada ba manyan na wancan lokacin sun yi kuskure don kawai su ci ma burin su. Wani yace shi kan shi Gwamnan da bazar su yake rawa don haka ya ji da dai aikin gaban sa na Shugabancin Jihar Kaduna.


[NAIJ Hausa]

Friday, July 21, 2017

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci


Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka 


  • A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala
  • Musulmai sun dauki wannan rana da muhimmanci
  • Ranar Juma'a na daya daga cikin Ranakun Idin Musulunci

A yau kuma mun koma zauren Addinin Musulunci ne inda mu ka tabo kadan daga cikin falalar wannan rana ta Juma'a. Akwai sunnoni da dama da ake so a aikata a wannan rana.

  1. Karbar addua
Ya zo a hadisin Bukhari da Muslim cewa akwai wani lokaci a wannan Rana da ba a maida addua da zarar mutum yayi ta. Wannan na daga cikin falalar wannan Rana.

  1. Rubuta lada
Duk wanda ya isa masallaci kafin Liman ya iso ya gabatar da huduba yana da matukar lada wanda Mala'iku ne za su sa shi cikin wani littafi. Iya saurin mutum iya ladar da zai samu Inji Manzon Allah SAW.

  1. Kariya daga Dujjal
Duk wanda ya karanta Suratul Kahf zai samu tsari daga fitinannen da zai zo a karshen zamani watau Dujjal. Haka kuma zai samu falala mai yawa har zuwa Juma’ar wata makon.
                                                                                                                                      


[NAIJ  Hausa]

Wednesday, July 19, 2017

Wani Dan wasan Ajax ya gamu da cutar kwakwalwa


Kwakwalwar wani Dan wasan kwallo ta buga ana cikin wasa 


  • Kwakwalwar wani babban Dan wasan Ajax tayi raga-raga
  • Babban Dan wasan ya samu wannan larura ne a filin wasa
  • 'Yan kwallon Duniya su na ta aika sakonnin jinya ga Dan wasan





Kwanaki kun ji labarin cewa wani Dan wasan Ajax ya kife ana tsakiyar kwallo. Yanzu dai ta tabbata cewa Kwakwalwar wannan Dan wasan ta samu matsalar da ba zai warke ba.

Kwanan nan mu ka samu labari cewa kwakwalwar Dan wasa Abdelhak Nouri na Kungiyar Ajax tayi dameji. Bisa dukkan alamu dai wannan ba karamar lalura bace wanda ba ma wasan kwallon kafar kadai za ta hana sa ba.




Kungiyar sa ta Ajax da ke kasar Holand dai wannan abu bai ma ta dadi ba. Haka sauran manyan 'Yan wasan Duniya sun aika sakon addu'o'in su ta kafafen zamani irin su Tuwita ga wannan mashahurin Dan wasa da Iyalin sa. 

Dan wasan tsakiyar na Ajax Abdelhak Nouri ya fadi ne bayan an kusa doka Minti 70 da take wasan da ake karawa ta Kungiyar Werder Bremen na kasar Jamus kwanaki.



[NAIJ Hausa]

Tuesday, July 18, 2017

Ashe akwai wanda ya fi Dangote kudi a Najeriya?




Ka ji Sanatan da ya fi Dangote arziki amma bai da ko gida a Abuja


  • Sanata Kabiru Marafa yayi da'awar kera Dangote dukiya
  • Sanatan yace a wajen sa wadatar zuciya ita ce Dukiya
  • Marafa yace idan kuwa haka ne to ya girmi Dangote a arziki





Sanata Kabiru Marafa na Jam'iyyar APC da ke Wakiltar Jihar Zamfara a Majalisar Dattawa yayi da'awar kera mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote dukiya inda yace shi na shi mizanin awon dabam.

Babban Dan Majalisar yace a wajen sa shi wadatar zuciya ita ce arziki amma ba tsabar kudi ba. Sanatan yace idan kuma wannan ake magana to shi hamshakin attajiri ne don kuwa yana da wadatar zuci kwarai.

Sanatan yace har yanzu hayan gida yake yi a Abuja kuma yace kashi 60% cikin 100% na abin da ya samu hannun mutanen da su ka zabe sa yake komawa. Snatan dai ya nuna cewa bai da handama ko kadan.





[NAIJ Hausa]

Sunday, July 16, 2017

Mutane 5 da su ka iya ganawa da Buhari a Landan


Mutane 5 da su ka kai wa Shugaba Buhari ziyara a Landan


  • Mun bi diddigi mun gano wasu daga cikin wadanda su ka iya ganawa da Buhari
  • Tun bayan tafiyar Shugaban kasa Buhari babu wanda ya san halin da yake ciki
  • Sai dai Matar sa da Mukadashin sa sun samu ganawa da shi a Birnin Landan


Mun bi diddigi daga Jaridu irin su The Nation mun gano wasu ha kadan daga cikin wadanda su ka iya ganawa da Shugaba Buhari tun bayan fitar sa Landan.


1.      Mukaddashin Shugaban kasa
Kun san cewa Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ma bayyana yadda su kayi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Landan inda su ka hadu na fiye da awa guda a daren Laraba.

2.      Uwargidan sa Aisha Buhari
Hajiya Aisha Buhari ta kai ziyara Landan kusan ba sau daya ba ma inda ta gana da Mijin na ta kuma ta kira ‘Ya Najeriya su cigaba da addu’a.

3.      Shugaban Hukumar DSS
Mallam Lawal Daura wanda shi ne Shugaban Hukuar DSS da ke kula da kare Shugaban kasar ya samu ganin Shugaban kasar.

4.      Ministan Ilmin Najeriya
Ministan Ilmi na kasa Malam Adamu Adamu yana cikin wadanda su ka samu ganin Shugaba Buhari tun bayan tafiyar sa. Alakar sa dai da Shugaba Buhari ba yau ta fara ba.

5.      Ministan Shari’a na kasa
Bayan Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu mun ji cewa Abubakar Malami wanda yake na hannun dama kuma Ministan shari’a ya samu ganin Shugaban kasa Buhari kwanaki a Landan kafin haduwar sa da Osinbajo.  



[NAIJ Hausa]

Saturday, July 15, 2017

Abin sha’awa: Osinbajo ya taya matar sa murnar cika shekaru 50



Matar Farfesa Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya 



  • Matar Farfesa Yemi Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya
  • Mukaddashin Shugaban kasar ya taya ta murna cikin dare
  • Farfesa Osinbajo yace yana alfahari da matar ta sa Dolapo



A safiyar yau ne Matar Farfesa Yemi Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya da haihuwa. Haka kuma Mijin na ta ya dauki lokaci inda ya taya ta murnar zagayowar wannan rana.

Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya taya Uwar ‘ya ‘yan ta sa 3 murna na musamman inda ya kawo mata ‘dan kek cikin dare lokacin yayin da ba tayi tsammani ba. Osinbajo yake cewa ita ce fika-fikan sa da yake tinkaho da su.

Shekaru fiye da 27 kenan da auren Farfesa Osinbajo da Dolapo wanda jika ce ta tsohon Firimiya na Kasar Yarbawa Marigayi Cif Obafemi Awolowo. Matar Shugaban kasa watau Aisha Buhari ta taya kawar ta murnar wannan rana.



[NAIJ Hausa]

Friday, July 14, 2017

Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N



TAKAMA DA MUSULUNCI



Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria

Daga Bakin Sheikh S.S Abubakar


Bayan shaidawa da gaskiya cewa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah mai girma, shi kadai yake bai da abokin Tarayya. Godiya da yabo sun tabbata a gare Sa, Shine mai iko kan komai. Muna shaidawa cewa lallai Shugaban mu Annabi Muhammadu SAW Bawan Allah ne kuma Manzon sa.


Bayan haka:
Duk wanda yake da lafiyayyen hankali to yana da abin gadara a rayuwa. Amma fa babban abin gadara shine addinin Musulunci wanda Allah ya yarda kuma ya zaba don shi ne mafificin ni’ima da mutum zai samu a cikin rayuwar sa kamar yadda yake fada a Ranar da aka kammala wannan addini. Allah SWT Yace ya cika n’ima a kan mu kuma ya zaba mana Musulunci ya zama addinin mu. Saboda haka Musulmi na gaskiya a ko yaushe yana takama ne da gadara da wannan ni’ima tare da aiki a lokutan sa ga wannan addini.

Bayin Allah wannan takama ba magana ce ta fatar baki ba, aiki ne tukuru in har mutum yana takama da wannan addini. Sai mutum ya dage ya mike yayi aiki tukuru don cin burin wannan addini na samun yardar Allah ta bin shiriyar Manzon Sa SAW a cikin dukkan wani motsi a rayuwa.

Samun yardar Allah Mai girma kan kasance ta hanyar kadaita Sa na dagewa da tsayawa kan Tauhidi da bin hukuncin Allah da nisantar abin da Ya hana. A yayin yin hakan dole mutum yayi kokarin tafiya tare da Iyalan sa ba wai shi kadai ba saboda wannan maganar ceto ne daga wuta zuwa Rahama. Allah SWT yayi umarni a Qur’ani cewa Ku tseratar da kawunan ku da Iyalan ku daga wuta wanda makamashin ta Mutane…Dole ne wannan ya ginu a bisa Imani da aiki na kwarai. Allah Madakaki yana cewa Wadanda su ka yi Imani da kuma aiki na gari za su samu Aljanna. Kuma dama Allah SWT yace duk wanda aka tsirar daga wuta zuwa aljanna, hakika ya rabota! Manufar wannan rayuwa dai ita ce bautawa Allah gwargwado kuma bissa yadda ya dace.

Babu wani dalili na gadara da wannan Addini matukar ba ayi istikama kan shari’ar Allah ba. Kuma wannan istikama ita ce bin tafarkin Allah mikakkiya kamar yadda duk Musulmi ke roko a cikin kowace Sallah. A kan wannan dandamali da ke tsakanin umarni da hani Musulmi na kwarai yake tafiya. Amma fa irin wannan tafarki na bukatar abokan tafiya don haka sai Musulmi ya san irin abokan tafiyar na sa. Allah SWT ya koyar da mu cewa mu nemi tafarkin da ba na wadanda aka yi fushi da su ko batattu ba!

A yayin da ake wannan tafiya kullum Musulmi dubawa zai yi ko su wanene abokan tafiyar sa kuma dole su zama masu imani da Allah kuma wadanda su ka tsaya cak da bauta bisa shiryar Manzo SAW tare da ado da halaye irin na Musulunci. A cikin wannan tafiya ta neman dacewar Allah SWT to Musulmi ya san irin mutanen da zai tafi tare da su. Mutanen na ba na kirki ba, sun san Mutanen su; Barawo ya san irin mutanen sa idan har satar za ayi, haka ‘dan fashi da duk wani mai barna. Ta ya mai imani da shiriya ya zama bai san Abokan tafiyar sa ba? Ya kamata Mai Imani idan har ka gan sa tare da Mutanen banza to sai dai larura, kullum yana so ya zama tare da masu gaskiya a matsayin majibinta. Allah yana cewa a Qur’ani mai girma Muminai maza da Mata, sashen su na tare da sashe. Haka kuma Kafirai su ma sashen su na tare da sashe, har sai sun rasa na su, za su dauki Mumuni. Munafukai kuwa Allah yace sashen su daga sashe yake gaba daya. Haka wannan ya zo game da Azzalumai yayin da Allah SWT yake Gatan masu Imani.

Jama’a kowa yana takama ne da abokan tafiyar sa. A duk wani al’amari sai mutum ya nemi abokan tafiyar san a kwarai; Daidai ga noma, Mutum kan nemi masu gaskiya ne da imani irin sa a matsayin abokan tafiya, ba a zuwa a dauko maha’inta marasa gaskiya wajen tafiya. Dukkan mai imani ya san abokan tafiyar sa. Saboda haka Bayin Allah ku tsaya wajen tsare addini; ka da ayi rauni ko bakin ciki wajen wannan jarrabawa.

Allah Madaukakin Sarki game da mai takama da addini sa yace: ‘Wa ya fi kyawun magana irin wanda yayi kira zuwa ga Allah yace kuma a tsaya a yi aiki na gari, a karshe kuma yace ina cikin Musulmi!’ Babu wanda ya fi wanda yayi wannan kirari kyawun magana. Jama’a ka da mu raina addinin mu wanda yayi mana tanadin rayuwa mai kyau a nan Duniya da kuma Lahira. Idan mun shiga baki ciki sai mu koma mu duba inda mu kayi sakaci wanda duk wannan amsa tana cikin addinin nan na mu. Lallai mu na cikin gadara da wannan addini mai albarka kuma mu san abokan tafiyar mu sannan ka da mu bari don rashin hangen nesa mu rungumi abokan tafiya na banza na daga kafirai da sauran masu fasadi.

Allah ya bamu ikon fahimtar AlKurani mai Girma da aiki da shi. Allah ya tserar da ni da k duka daga azaba mai radadi ya shiga da mu Aljanna. Allah ka dada tsira ga Annabi Muhammad SAW da iyalan sa da Halifofin sa, da sauran wadanda suka bi su da kyautatawa. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmai ka buwayar da Musulmai da wannan addini na ka. Allah ka sa sahun Musulmi ya zama guda ka kuma raya wannan kasa ta mu ka kare mu. Allah ka sa albarka bisa abubuwan da ka azurta mu da su. Allah ka warkar da marasa lafiya musamman Shugaban wannan kasa ka kuma jikan wadanda su ka rasu.  Allah ka ba mu zama lafiya kayi mana maganin Azzalumai da Fajirai ka tabbatar  mana da alheri Duniya da Lahira.

-Mallam Salihu S. Abubakar, Masallacin Islamic Trust of Nigeria, ITN, Zaria.




Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria

Twitter: @Ya_waliyyi

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...