Fadar
Shugaban kasa ta tabbatar da cewa an yi wa Shugaba aiki a asibiti
- Rashin lafiya ta tasa Shugaban kasar Benin a gaba
- An yi wa Shugaban aiki a Birnin Faris
- Shugaba Talon dai ya dade yana jinya
Shugaba Partrice Talon na Benin na fama da rashin lafiya. Abin har ya kai an yi
wa Shugaban aiki har sau biyu. Kusan wata guda kenan
Shugaban kasar ba ya Gari. Haka dai shi ma Shugaba Buhari na Najeriya na kwance a Ingila.
Shugaba Partrice Talon
na Kasar Benin na fama da rashin lafiya na kusan wata guda wanda har ta kai aka
kai shi Birnin Faris domin ya ga Likita. Rahoto na zuwa cewa dai har ta kai an
yi wa Shugaban aiki a jiki har sau biyu.
An dai shafe wata guda
kenan Shugaban kasar na Benin na Kasar Faransa inda ake lura da shi. Fadar
shugaban kasar da farko dai ta bayyana cewa ba shakka an yi shugaban aiki wanda
kusan duk ana sa rai cewa an dace.
Kun ji cewa haka kuma a Najeriya
Shugaba Buhari Muhammadu ya koma Asibiti a can Landan tun kwanaki. Farfesa Yemi
Osinbajo ke rike ragamar kasar har lokacin da Ubangiji yayi shugaba Buhari ya
dawo.
Ya Allah Ka BA buhari lafia kasa kaffara ne Ya ArRahmanr Raheem.
ReplyDelete