Saudiya
ta aikowa Najeriya ton 200 na kayan shan ruwa
– Saudi ta aikowa Najeeriya tumin dabino domin shan ruwa
–
Ofishin Jakadancin kasar ya tabbatar da wannan
– Ministar harkokin kasar waje ta
godewa Saudiya da karamci
- Za a rabawa ‘Yan gudun Hijira dabinon azumi
- Saudi ce dai ta aikowa Najeriya ton 200 na dabino
- Akwai dai alaka mai kyau tsakanin kasashen biyu
Ofishin
Jakadancin Saudiya a Najeriya ta bakin Dr. Yahya Ali Mughram ya bayyana cewa
kasar ta aikowa Najeriya ton 200 na dabino domin Musulmai su samu abin buda
baki. Ana dai shiri tsakanin Najeriya da kasar mai tsarki.
An
dai mikawa Ministar harkokin kasar waje Hajiya Khadija Bukar Abba wannan kayan
alheri inda tayi godiya ga Kasar Saudiya ta kuma yi alkawarin raba kayan ga
musamman ‘Yan gudun Hijira da ke Yankin Arewa maso gabas.
Kun
ji cewa Sanatoci sun nemi rage kudin kujerar aikin Hajji na wannan shekarar
kuma a daina karbar kudin abinci. Kudin kujerar aikin Hajjin bana dai ya haura Miliyan
daya da rabi. Kwamitin harkokin kasar
waje dai zai duba lamarin bayan kukan da Jama’a su kayi.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment