Thursday, June 29, 2017

Yau Najeriya za ta fitar da doya kasar waje



Najeriya ta fara fitar da doya zuwa Kasar China


  • Yau Najeriya ta fara fitar da doya zuwa Kasar China
  • Duk Duniya babu inda ya kai Najeriya noman rogo da doya
  • Gwamnatin Shugaba Buhari ta dage wajen harkar noma



Hakika Shugaba Muhammadu Buhari ya dage wajen ganin an koma noma a kasar nan. Yanzu haka Kasar Najeriya za ta fara fitar da doya a yau dinnan da mu ke magana. Tuni kasashen China da sauran su suka nemi a kawo masu doya daga kasar nan.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dage wajen harkar a kasar nan wanda yanzu har ta kai yau za a fara fita da doya zuwa kasar waje. Ministan gona na kasar Cif Audu Ogbeh ya tabbatar da wannan kamar yadda mu ka samu labari.

Kasar China watau Sin dai tayi odar wannan kaya wanda zai ba Najeriya damar samun kudin kasar waje. Duk Duniya babu inda ya kai Najeriya noman rogo da doya musamman ta bangaren Arewa maso tsakiya na kasar.

A bara an noma sama da ton miliyan biyu na shinkafa a Najeriya. Yanzu dai abin da Najeriya ta ke fitarwa ya fi karfin abin da ake shigo da shi wanda shi ne manufar Gwamnatin Shugaba Buhari.



[NAIJ Hausa] 


No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...