Yadda ‘Yar da ba kowa ba ta auri ‘Dan wanda ta fi kowa kudi a Duniya
- Ko
kana da labarin wata mata Folorunsho Alakija?
- Alakija
na cikin matan da su ka fi kowa kudi a tarihin Duniya
- Kwanan nan ‘Dan ta ya kashe kusan Dala Miliyan 5 wajen auren sa
Folarin Alakija ya tada
kusan Biliyan 2 wajen bikin aure. Folarin ya auro wata ‘Yar
kasar Iran ce da ke zaune a Ingila. Asali Amaryar sa Nazanin ba
‘yar gidan kowa bace a Duniya.
Folarin Alakija wanda ‘Da ne
wajen matar da duk Duniya da wuya a samu bakar mace da ta taba kera ta dukiya ya
auri Nazanin Jafarian Ghaissarifar wata ‘Yar asalin kasar Kasar Birtaniya. A bikin dai an kashe kudi sama da Naira biliyan 2.
Nazanin
Jafarian tayi Digiri kan fannin likitanci da kuma wata difloma a harkar shari’a sannan kuma tana aikin kwalliya ne da gayu har ta kan yi aiki da Iyalan Kardashians da su kayi fice a Duniya.
An yi wannan kasaitaccen
biki ne a Fadar Blenhim da ke Garin Oxfordshire a Kasar Birtaniya. Asalin
Nazanin dai ba masu wadata bane don kuwa Mahaifiyar ta sai da tsiyace ma bayan
dawowar su Ingila inda su ke zaune hannun ubangiji.
Shekarun baya dai Mahaifiyar
Angon Alakija ta zarce Attaajira Oprah Wimfrey ta Amurka kudi. Alakija mai
shekaru 66 ta mallaki sama da Dala Biliyan biyu.
[Muhammad Malumfashi ya fara kawo wannan rahoto a NAIJ Hausa]
<script async src="//pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js"></script>
<script>
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({
google_ad_client: "ca-pub-4526893122328023",
enable_page_level_ads: true
});
</script>
<script async src="//pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js"></script>
<script>
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({
google_ad_client: "ca-pub-4526893122328023",
enable_page_level_ads: true
});
</script>
No comments:
Post a Comment