Uwa ta rikice: Diyar ta na soyayya
da tsohon Mijin ta
– Wata yarinya
ta kama soyayya da Mijin Mahaifiyar ta
– Sai daga baya Mahaifiyar wannan
yarinya ta gano haka
– Wannan yarinya
tayi shekaru 20 tana kiran wannan mutumi ‘Baba’
Wasu Ma'aurata a Kasar Ingila
- Wani abin da wasu su ka kira kayan assha ya faru a can kasar waje
- Wata Yarinya ce mai shekaru 31 ta koma son Bazawarin Mahaifiyar ta
- Jaridar Daily Mail ce ta rahoto wannan labari
Mun samu labari daga Jaridar Daily Mail cewa wata
mata ta rikice yayin da Diyar cikin ta ta buge da auren tsohon Mijin ta. Wannan
yarinya dai ta zauna a matsayin agola a gidan wannan mutumi na fiye da shekaru
20.
Wannan abu dai ya ba matar mamaki yayin da Bazawarin
na ta ya aure Diyar da ta haifa a waje kafin ta aure sa. Ta dai shigo gidan ne
da wannan yarinya lokacin tana shekara 11 a Duniya. Matar tace sam wannan abu
bai mata dadin ji ba.
Haka kuma za ku ji cewa rahotanni daga Kasar Sifen na nuna cewa
babban Dan wasan nan na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya samu jarirai tagwaye
masu suna Mateo da Eve. Ko wacece uwar tagwayen?
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment