An kama tsohon Dan wasan Real Madrid da laifin rashin biyan haraji
- Dan wasan PSG Di-Maria bai biya wasu kudin
haraji ba
- Angel Di-Maria ya tabbatar da
bakin sa cewa bai da gaskiya
- Sai dai da wuya Di-Maria ya shiga
gidan kurkuku wannan karo
Bayan
Cristiano Ronaldo an kara samun wani Dan wasa da laifin haraji. Dan
wasan gaba Di-Maria na Kasar Ajentina bai da gaskiya. Ta
tabbata da bakin Dan wasan cewa bai biya wasu kudi ba lokacin yana wasa a Sifen.
An kama tsohon Dan wasan gaban Real Madrid da Manchester United Angel Fabian
Di-Maria da laifin rashin biyan kudin haraji a lokacin da yake kasar Sifen
kamar yadda mu ke samun labari daga Jaridun Turai.
Di-Maria
ya tabbatar da kan sa cewa akwai wasu kudi har na Dalar Euro Miliyan £1.14 da ya ki
biya kamar yadda doka ta tanada. Hakan dai ta sa aka yanke masa daurin shekara
daya a gidan maza. ‘Dan wasan ba zai yi zaman yari ba tun da wannan ne karo na
farko da aka kama sa da laifi.
Ku
na da labari cewa Dan wasa shi ma Cristiano Ronaldo na shirin barin Real Madrid
bayan an fara zargin sa da kin biyan haraji. Shi ma tsohon Kocin
na sa Jose Mourinho bai sha ba.
[NAIJ Hausa]
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment