Ana
zargin Dan wasan Real Madrid da laifin haraji
– Ana zargin Dan wasan Duniya Ronaldo da laifin rashin biyan haraji
– Hukuma za ta tuhumi ‘Dan wasan
da wannan babban laifi
– Akwai yiwuwar Dan wasan bai biya
sama da Dala Miliyan 16 na haraji ba
Ana
iya kama babban Dan wasa Ronaldo da laifin haraji. Haka
dai aka yi da Dan wasa Lionel Messi. Duk 'Yan wasan Duniya babu wanda ya kai Dan kwallon karbar albashi a halin yanzu.
Ana
zargin Babban Dan wasan kwallon kafar nan na Duniya Cristiano
Ronaldo da rashin biyan kudin harajin da ke kan sa na sama da Dala Miliyan 16. Kwanaki
Kotu ta yankewa Lionel Messi daurin watanni 21 bayan an same sa da irin wannan
laifi na kin biyan haraji.
Akwai
zargin cewa Dan wasan bai bayyana asalin abin da yake samu ba wanda ta hakan ne
ya biya kasa da abin da ya kamata ya Hukuma a matsayin kason haraji. Ronaldo
dai na samun kudi ta wasu hanyoyin iri-iri ban da albashin sa irin su talla da
kudin rigar wasa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment