Hudubar Idi: Limamin ABU yayi kira ga ‘Yan Najeriya
- Babban Limamin
masallacin Jami’ar A.B.U yayi kira ga ‘Yan kasa
- Sheikh Salihu Abubakar ya nemi ‘Yan Najeriya su daina
dogaro da Gwamnati
- Malamin yayi wa Kasar Najeriya da sauran Jama’a addu’a
Sheikh Salihu Abubakar ya
kira Jama’a su tashi tsaye wajen kawo gyara. A cewar babban Shehin ba
dole Gwamnati ce za tayi gyara ba. Malamin yayi wa kasa da
Shugaba Buhari addu’a.
Babban Limamin masallacin
Jami’ar A.B.U watau Ahmadu Bello Sheikh Salihu Santalma Abubakar yayi kira ga ‘Yan
Najeriya da su tashi tsaye kuma su daina dogara ko-ca-kam kan Gwamnatin Kasar. Haka
kuma Malamin yayi wa Shugaban kasa da
Jama’a duk addua.
Babban Limamin
masallacin Jami’ar A.B.U yayi kira ga ‘Yan kasa
Shehin Malamin yayi kira da ‘Yan
kasa su dage a duk matakin da su ke na kawo gyara. Sheikh S.S Abubakar ya nemi
Jama’a da su kawo gyara domin za a tambaye su duk inda su ka samu kan su domin
kawo gyara na gari a cikin al’umma.
Kun ji cewa Shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya ta bakin mai ba shi
shawara kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu. Shugaban Kasar yayi
godiya inda ya kuma nemi a zauna lafiya a Najeriya.
No comments:
Post a Comment