Wednesday, June 21, 2017

Babu maganar tursasawa Jama’a Musulunci a Najeriya


Gwamnatin Tarayya ta kauda zargi na yunkurin Musuluntar da Najeriya


  • Gwamnatin Tarayya ta kauda duk wani zargi game da maganar wasu Fastoci

  • Wasu na ganin akwai makarkashiya na tursasawa ‘Yan Najeriya Musulunci

  • Gwamnatin kasar dai ta yi watsi da wannan maganar kamar yadda za ku ji




Wasu na ikirarin cewa an soke ilmin addinin Kirista daga darussan Sakandare. Haka kuma ana yada cewa an saka larabci da ilmin addinin musulunci. Ma’aikatar ilmi dai ta wanke duk wannan zargi dalla-dalla.

Gwamnatin Tarayya ta musanya zargin da ke yawo na cewa an soke ilmin addinin Kirista daga darussan makaruntun Sakandare. Gaskiyar maganar dai ita ce tun lokacin tsohon Shugaba Jonathan aka fara wani garambawul a tsarin ilmin kasar.

Yanzu haka dai an maida darusan addinin musulunci da na kiristanci wuri guda inda kowane dalibi zai dauki wanda ya dace karkashin wani darasi na dabam. Haka kuma an kawo yaren Larabci tare da na Faransanci ga duk mai bukata amma babu dole a lamarin.

Bayan Kungiyar CAN ta Kiristoci, Fasto Johnson Solomon yace Gwamnatin Buhari na kokarin murkushe addinin Kiristanci a kasar nan. Faston yace an soke ilmin addinin Kirista daga darasin makarantu kuma aka bar na Arabi da Musulunci. Wannan magana dai ba daidai ba ce sam.

Idan ba ku manta ba a cikin kwanan nan ne aka kai wani mugun hari a Garin Mambila da ke Jihar Taraba inda aka kashe Fulani da dama bayan an kona gidajen su. Har yanzu Gwamnatin Jihar da ta Tarayya ba tayi wa kowa jaje ko ta’aziyar Allah ya kyauta ba.





[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...