Sallar
Idi: Sakon Shugaba Buhari ya kwantar da hankalin ‘Yan Najeriya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sako ga
mutanen Najeriya
- Ana ma dai sa ran Shugaban kasar ya kusa dawowa
Najeriya
- Mun ji kishin-kishin din cewa dimuwa ta fara kama
Shugaban kasar
Shugaba Buhari ya aiko sakon
Sallah ga ‘Yan Najeriya ta bakin Garba Shehu. Shugaban Kasar yayi godiya
inda ya nemi a zauna lafiya a Najeriya. Masu nazari kuma sun
tabbatar da cewa muryar shugaban ce ba kage ba. Wannan dai ya sa hankalin da dama na kasar ya kwanta.
Yayin da wasu ke maganar
cewa rashin lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara tabarbarewa sai ga
shi ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya inda yayi kira a cigaba da zama
lafiya a kasa tare da addu’a domin sauke nauyin da ke kan Shugabannin.
Shugaban kasar dai ya godewa
‘Yan Najeriya game da irin addu’o’in da aka rika masa yayin da yake fama da
jinya. Masu nazari dai sun ce ba shakka cewa muryar Shugaban kasar ce don kuwa
ya taba abubuwan da su ke faruwa a kasa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment