Yawan
mutanen Najeriya zai karu nan da 2050
- Harsashe ya nuna cewa yawan mutanen Najeriya zai lula
- A haka ma dai Najeriya ce ta 7 wajen yawa a Duniya
- Zuwa shekarar 2050 kasar za ta kere Amurka
Yawan mutanen Kasar Najeriya
kara karuwa kurum yake yi. Nan da wani lokaci Najeriya
za ta zama ta uku wajen adadin Jama’a. Kasar China da kuma India ne
sahun gaba wajen yawan al’umma a Duniya.
Wani harsashe da wata Hukuma
da ke kula da yawan Jama’a na Duniya tayi ya nuna cewa Najeriya za ta kerewa
Kasar Amurka wajen yawan mutane nan da shekarar 2050. Hakan na nufin Najeriya
za ta zama ta uku wajen yawan Jama’a a kaf Duniya.
Zuwa wannan lokaci dai yawan
haihuwar da ake samu a Nahiyar Afrika zai ribanya wanda ake samu a halin yanzu.
Zuwa shekarar 2020 adadin Jama’an Duniya dai zai kusa Biliyan 10. Yanzu dai
adadin mutanen Duniyar yak era mutum Biliyan 7.6.
Kasashe irin su Najeriya da
China watau Sin, Indiya, Indonesiya, Fakistan da Amurka su na cikin wadanda su
ka fi yawan al’umma a Duniya. Najeriya na fama da matsaloli daban-dabam irin na talauci, jahilci, kuncin rayuwa, yawan laifuffuka, ta'addanci da matsalar zamantakewa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment