Cristiano Ronaldo ya samu lambar
yabo daga Lionel Messi
– Babban Dan
wasan nan Lionel Messi ya jinjinawa Ronaldo
– Yake cewa Cristiano Ronaldo ba
karamin Dan wasa bane
– Dan wasan yace
Ronaldo na taimaka sa a wasan sa
- Dan wasa Ronaldo ya samu jinjina daga Messi na Barcelona
- Lionel Messi yace ba shakka Ronaldo babban Dan wasa ne
- ‘Yan wasan dai sun yi kaurin suna a Duniya tun shekarar 2008
Idan kwallon kafa ake magana babu irin Dan wasan nan
Lionel Messi na Barcelona na Barcelona da Cristiano Ronaldo na Real Madrid. Wannan
karo Messi ne da kan sa yake yabawa Dan wasan gaban na Real Madrid.
Dan wasa Messi yake cewa Ronaldo hamshakin Dan wasa
ne wanda ake ji da shi a Duniya. A cewar Messi, shi da Ronaldo sun taimaka
wajen gyarawa junan su kwallon da su ke bugawa inda kowa yake Sarki a gidan sa.
Kwanaki Ronaldo na Madrid yace alakar sa da Dan wasa
Lionel Messi ta kirki ce ya kuma kara da cewa kwallon Dan wasan na burge sa don
kuwa ya san leda. Sai dai yace bai so ana hada shi da Dan wasan.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment