Wednesday, June 7, 2017

‘Yan kwallo 5 da su ka fi kowa albashi a Duniya



‘Yan wasan da su ka fi kowa kudi a Duniya



– Babban Dan wasan Real Madrid Ronaldo ya fi kowa albashi 


– A bana kurum Ronaldo ya samu kudi har Dala Miliyan 88


– Lionel Messi ne ya zo na biyu a jerin 




Duk Duniya babu Dan wasan da ya kai Ronaldo albashi

  • Mujallar Forbes ta fitar da wadanda su ka fi kowa albashi cikin ‘Yan wasa
  • Dan wasa Cristiano Ronaldo dai ya kerewa kowa a maganar kudi
  • Cristiano Ronaldo ne Dan wasan Duniya yanzu haka

A jerin ‘Yan wasan kwallon da su ka fi kowa albashi a Duniya Cristiano Ronaldo ne kan gaba inda a bana kurum ya tashi da sama da Dala Miliyan 88. Dan wasa Lionel Messi na Barcelona ya hada Dala Miliyan 81 a wannan shekara.

Sauran ‘Yan wasa irin su Neymar Jr na Barcelona, da kuma Gareth Bale na Real Madrid da ma Zlatan Ibrahimovich na Manchester United su na cikin wadanda su ka fi kowa albashi a Duniya a wannan shekara. 

Kungiyar Real Madrid ce ta lashe kofin Champions league na 2017 bayan ta doke Juventus da ci 4-1 a Birnin Cardiff. Ronaldo ya kara nuna cewa ya cika gwarzo inda ya jefa kwallaye biyu. Dan wasa Ronaldo ne dai ya kara gamawa da kwallayen da su ka fi na kowa a Gasar.






[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...