Kasar Argentina za ta cika makil a ranar bikin auren Messi
- Auren Dan
wasan Barcelona Lionel Messi ya karaso
- Za dai a ga cincirindo a kauyen
Dan wasan a Kasar Argentina
- Dan wasan Real
Madrid Morata zai yi aure wannan makon
Dan wasan Duniya zai yi aure: Kauyen su Messi zai yi irin cikar da bai taba yi ba
Cikin wannan watan dai ‘Yan wasa da dama za su yi
aure. Kwanan nan Dan wasan da ke tsaron ragar Kungiyar Bayern Munchen watau Manuel Nueuer ya shiga daga ciki. Irin su Lionel Messi na shirin biyo shi kwanan nan.
A karshen wannan watan Dan wasa Lionel Messi na Barcelona zai zama Ango a Birnin Rosario da ke Kasar Argentina. Messi zai auri sahibar sa da su kayi shekara da shekaru tare tun su na yara Antonella Roccusso.
Haka kuma 'Yan wasan Real Madrid har 3 za su angonece. Daga ciki Alvaro Morata zai auri
Budurwar sa Alice Campello a wannan Asabar din mai zuwa. Haka ma Lucas Vasquez da Mateo Kovacic na Kasar Kuroshia.
Kwanaki kun ji cewa babban Dan wasan nan na Real
Madrid Cristiano Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve a Amurka. Ko da
yake dai har yanzu kamar ba a san Mahaifiyar 'Ya 'yan ba kamar yadda har yau ba a sa wanda ta haifa masa 'Dan sa na farko ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment