Danjuma da Danjumai: ‘Yan Darika da
‘Yan Shi’a ‘Yan uwa ne Inji Shehun Tijjaniyya
- Babban Shehin Darika Dahiru
Bauchi yayi magana game da Shi’a
- Shehun Darikar yace su da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwan juna ne
- Dahiru Bauchi yace sun yi tarayya
da ‘Yan Shi’a wajen son Manzon Allah
Sheikh
Dahiru Bauchi yace ba su fada da ‘Yan Shi’a. Shehin
ya fadi haka ne yayin da aka kai masa ziyara. ‘Yan
Shi’a da Dariku su na kaunar Manzo Inji Shehin. Wasu 'Yan Shi'a ne su ka kai masa ziyara a Kano.
Babban
Shehin Darika Tijjaniyya Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa ‘Yan tarika da
‘Yan Shi’a duk jirgi daya ne ya dauko su don kuwa sun yi tarayya wajen kaunar
Manzon Allah Muhammadu SAW.
Wasu
‘Yan Kungiyar Shi’a ne dai su ka kai masa ziyara bayan ya kammala karatun
tafsirin bana. Ya yabawa ‘Yan Shi’ar wanda yace duk sun hadu wajen soyayyar
Manzon Allah da iyalan sa. Shehin dai ya yabawa wannan ziyara da aka kai masa a
Kano.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment